Ɓaraka tsakanin ′ yan tawayen Siriya | Labarai | DW | 25.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ɓaraka tsakanin ' yan tawayen Siriya

Manyan ƙungiyoyin na 'yan tawaye na ƙasar masu kishin addini sun yi watsi da duk wata ƙungiya da ke a ƙasashen waje da cewar za ta wakilcesu.

A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da ƙungiyoyin kusan guda 13 suka saka hannu akai, ta ce ko kaɗan ba su amince ba kungiyoyin, su yi magana da sunan su ba, sannan kuma sun ce shari'ar addinin islama ita kaɗai ce hanya ta doka a garesu.

Ƙungiyoyin dai sun haɗa da Free Syrian Army da Al-Nusra da dai sauransu. A yau dai wasu ƙwararru na Majalisar Ɗinkin Duiniyar suka isa a ƙasar ta Siriya domin ci gaba da yin bincike dangane da zargin yin amfani da makamai masu guba a kusa da birnin Damascus.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu