Ƙurdawa sun ƙwace dam ɗin Mosul | Labarai | DW | 17.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙurdawa sun ƙwace dam ɗin Mosul

rahotannin da ke zo mana daga Iraƙi na cewar dakarun Ƙurdawa sun yi nasarar ƙwace dam ɗin da ke a arewacin ƙasar bayan mummunar hare-hare ta jiragen sama da suka kai.

Wani babban jami'in gwamnatin Ƙurdawa ya tabbatar da cewar dakarunsu,sun karɓe iko da dam ɗin wanda ke samar da ruwa da kuma wutar lantarki ga ɗaukacin yankunan arewacin yankin.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da sojin Amirka suka kai farmaki ta sama har sau tara kan mayaƙan IS ɗin daura da dam din na Mosul da kuma garin Irbil da ke yankin na Kurdawa, inda rahotanni ke cewar hare-haren sun lalata makaman 'yan fafutukar. Wani mazaunin yankin Nayem Jassem ya ce Ƙurdawan sun makara saboda masu jahadin sun riga sun tafka mummunar ɓarna inda ya ce sun kashe ɗarurruwan jama'a.

Maallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu