Ƙungiyar Save the Children ta ce yara na cikin mawuyacin hali a Siriya | Labarai | DW | 13.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar Save the Children ta ce yara na cikin mawuyacin hali a Siriya

Yara kamar miliyan biyu ne 'yan ƙasa da shekaru 18 ke fuskantar gallazawa, kana kuma suna fama da cututtuka da rashin abinci sakamakon yaƙin ƙasar.

Ƙungiyar Save the Children da ke fafutukar kare hakin kananan yara, ta ce yaƙin da ake yi a ƙasar Siriya tsakanin 'yan tawaye da ke neman kifar da shugaban ƙasa Bashar al-Assad da sojojin gwamnati na zaman babban ƙalubale ga rayuwar yara ƙanana.

A cikin wani rahoton da ta baiyana ƙungiyar ta ce yara kamar milyan biyu ne ke fama da rashin samun isasshen abinci da cututtuka da auren dole, da kuma ruɗewa a yaƙin da kawo yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 70. Rahoton ya ce kashi biyu bisa uku na yara da aka yiwa tambayoyi, sun ce an raba su da iyayensu, yayin da yaro daya cikin uku ke cewar ya fuskanci takurawa. Ana dai zargin dakarun gwamnatin Siriya da na 'yan tawaye da laifin aikata ayyukan asha a kan jama'ar ƙasar galibi farar hula.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal