′Ƙungiyar M23 ta ce za ta janye daga Goma | Labarai | DW | 27.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Ƙungiyar M23 ta ce za ta janye daga Goma

Amma fa bisa sharuɗan da ta gindaya wa gwamnati, na sako bursunan siyasa tare da rusa hukumar zaɓe ta ƙasar

Ƙungiyar'yan tawaye ta M23 da ke da iko da yanki arewa maso gabashin Kwango ta ce a shirye ta ke ,ta janye da dakarunta daga garuruwan Goma da kuma Sake tare da fara yin shawarwari da shugaba Josephe Kabila amma fa bisa wasu jerin sharuɗa.

Yan tawayen sun ce tilas ne gwamantin jamhuriyar dimokaradiyyar kwango ta sako bursunan siyasar da ta ke tsare da su ,tare da rusa hukumar zaɓe ta ƙasar;to sai dai babban kwamanda dakarun kwangon Francpois Olenga ya ce suna jiran samu ummarni ne kwai domin kutsa kai cikin goma.Ya ce'' ba zamu tsaya ba abokan gaba su yi yadda suke so da mu, ya ce abin ya ishemu a kwai maciya amana da masu kawo masu dauki''.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi