Ƙungiyar Ansar Dine ta rabu gida biyu | Labarai | DW | 24.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar Ansar Dine ta rabu gida biyu

Wasu ya'yan ƙungiyar sun ce sun ware, kuma sun yi shelar yaƙar ta'adanci tare da yin kira ga hukumomin Paris da na Bamako da cewar a buɗe tattaunawa

An ba da rahoton cewar ɗaya daga cikin ƙungiyoyin yan tawayen ukku na ƙasar Mali masu kishin addini waɗanda suka mamaye yankin arewacin ƙasar kafin sojojin Faransa sun watsa su wato Ansar Dine ta rabu gida biyu.Yan aware na ƙungiyar sun girka wata sabuwar ƙungiyar mai fafutuka da ake kira da sunnan MIA Mouvevement Islamique de Lazawad.A cikin wata sanarwa da ta baiyana ƙungiyar ta yi allah wadai da aikin ta'adanci tare da cewar a shirye ta ke ta yaƙi ta'adanci.Sanan kuma ta yi kira ga hukumomin Mali da na Paris da su dakatar da buɗe wuta domin soma tattaunawa.

Ƙungiyar ta ita ce ke riƙe da garin Kidal wanda ke da ratan kilimta 1500 daga Bamako.Wannan sanarwa dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ƙungiyoyin kare hakin bil addama suka buƙaci da soma gudanar da bincike akan sojojin Mali waɗanda suke zargi da aikata ta'asa akan farar hula.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu