1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙoƙarin tabbatar da tsaro a Najeriya

Usman ShehuMay 13, 2014

Dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa a ƙaramar hukumar Kachia, na kawo tarnaƙi ga rayuwar al'ummar yanki a daidai lokacin da Ƙungiyar Boko Haram ta ke tsare da 'yan matan Chibok.

https://p.dw.com/p/1BytB
Nigeria Goodluck Jonathan
Hoto: AFP/Getty Images

Kimanin kwanaki biyu ke nan da gwamnatin Kaduna ta sanya dokar hana zirga-zirgan Jama'a na tsawon sa'o'i 24 a ƙaramar hukumar Kachia da ke a yankin kudancin Kaduna. Tun bayan ɓarkewar wani munmunar rikicin addini da ya auku a ranar Lahadin da ta gabata ,al'amarin da ya janyo salwantar rayuka da ƙone-ƙonen Coci-coci da Masallatai da gidaje da dama.

Dokar ta ɓacin na kawo cikas ga rayuwar al'umma a garin Kachia

Wannan yanayi dai na dokar ta ɓaci a yankin na kawo damuwa ga al'ummar yankin kamar dai yadda wasu jama'ar ke yin ƙorafi, waɗanda ke kokawa da ƙarancin abinci da zaman ɗar-ɗar da zullumi da kuma ke buƙatar gwamnatin ta hanzarta sassauta dokar don ba su damar zuwa neman abinci da sauran abubuwan na buƙata.

Nigeria Soldaten Militär Boko Haram
Hoto: picture-alliance/dpa

Tuni dai ƙungiyoyin da ke fafatukar ci-gaban al'umma da Shugabannin Siyasa da masu faɗa a ji suka fara mayar da martani wanda suke yin Allah Wadai da lamarin kamar yadda Pastor Yohanna ya bayyana.

''Musulmai da Kiristoci na cikin wani mawuyacin hali sakamakon wannan tashin hankali, akwai buƙatar samun fahimtar juna domin tabbatar da zaman lafiya.''

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da wasu rahotannin da wakilanmu na Abuja da Filato da Niger suka aiko mana a kan dambarwar da ake faman yi ta fafutuka tun bayan da aka sace ' yan matan Chibok.

Mawallafi : Ibrahima Yakubu
Edita : Abdourahamane Hassane