Ƙasashen duniya na shirin kai wa Siriya yaƙi | Siyasa | DW | 28.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ƙasashen duniya na shirin kai wa Siriya yaƙi

Duk da ma cewar Majalijar Ɗinkin Duniya ba ta ba da izinin kai wa Siriya hare-haren ba, Amirka da sauran ƙawayanta na shirin fara kai farmakin.

A panel of journalists and others addresses a United Nations Security Council meeting on the protection of civilians in armed conflict and the protection of journalists, Wednesday, July 17, 2013 at U.N. headquarters. Panelists included U.N. Deputy Secretary-General Jan Eliasson, Richard Engel of NBC, Somali journalist Mustafa Haji Abdinur from Radio Simba and Agence France Presse, Iraqi journalist Ghaith Abdul-Ahad from the Guardian, and Associated Press Executive Editor Kathleen Carroll, who is vice chair of the board of the Committee to Protect Journalists. (AP Photo/Mary Altaffer)

Sitzung UN-Sicherheitsrat Gewalt gegen Journalisten

Mako daya bayan hare- haren makamai masu ɗauke da guba da aka kai a kusa da birnin Damascus ,yanzu haka mayan sefetocin Majalisar Ɗinkin Duniya, na can na ci ga da yin bincike, domin samun shaidu. Sai dai kuma yunƙurin da ƙasashen duniyar suke shirin yi na afkawa Siriya da yaƙi ya saɓama dokar ƙasa da ƙasa.

Ƙasashen duniyar na shirin yin fatali da Majalisar Ɗinkin Duniya.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya shi ka ɗai ne ke da hurumin ba da izzinin ɗaukar irin wannan mataki. To sai dai ƙasashen Rasha da China waɗanda ke da kujerun dindin a majalisar na iya kawo tarnaƙi ga shirin ta hanyar hawa kujerar naƙi saboda rashin amincewa da kai wa Siriya yaƙin.

Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da Amirka ta kan ɗarma ɗamarar yaƙi ba tare da amincewar MDD ba, a shekarun 2003 shugaba George W Bush na Amirka tare da haɗin gwiwar Ingila ya yi kira ga wasu ƙasashen duniyar domin kifar da gwamnatin Saddam Hussein kan hujjar da ba a tabbatar cewar Iraki ta mallaki makamai na ƙare dangi na nukliya.

Shin ko wannan yaƙi na Iraki zai iya zama iri ɗaya da na Iraƙi

WASHINGTON, DC - AUGUST 26: U.S. Secretary of State John Kerry delivers a statement about the use of chemical weapons in Syria at the Department of State August 26, 2013 in Washington, DC. Kerry said that chemical weapons had been used to kill scores of people during the ongoing civil war in Syria and that the government of President Bashar al-Assad had used shelling to destroy the evidence. (Photo by Chip Somodevilla/Getty Images)

John Kerry ministan harkokin waje na Amirka

A lokacin babban sakataran Amirka Collin Powell ya ce sun gabatar da wasu shaidu ga Majalisar Ɗinkin Duniyar a kan zargin,Abin da ministan harkokin waje na Jamus na waccan zamani Joschka Fischer ya ce ba su gamsu ba da bayyanan ba, abin da kuma ya riƙa kallo a matsayin babban kuskure har lokacin da ya janye daga harkokin siyasa.

A na kamanta irin abin da ya faru a Iraki da yanzu halin da ake ciki a Siriya, to amma wani babban hafsan soji na ƙasar Jamus Manfred Eisel ya ce yaƙin da ya faru a Iraki ba za a iya kamanta shi ba da abinda ke faruwa a Siriya sai dai watakila da yaƙin Kosovo

Ya ce : ''Kwamitin tsaro na MDD a lokacin ya fito ƙarara ya yi baiyani dangane da kisan ƙare dangi na ƙabilun da aka yi a Kosovo da kansa. Kuma duk da yadda Rasha ba ta amince ba a kai farmakin, rundnar NATO ta yanke shawarar kai hare-hare ta jiragen sama.''

Ana da fargaba saboda a kan ƙin amincewa da Rasha da China suka yi na kai hare-haren

Russia's Foreign Minister Sergei Lavrov attends a news conference after his meeting with Moroccan counterpart Saad-Eddine Al-Othmani in Moscow June 28, 2013. Lavrov said on Friday Russia was committed to arranging a peace conference on the Syria conflict but other countries and groups were complicating matters by trying to set preconditions. REUTERS/Alexander Demianchuk (RUSSIA - Tags: POLITICS)

Sergei Lavrov ministan harkokin waje na Rasha

Za a iya cewar an take hakkin bil addama a Kosovo wanda kuma sune dalilan da suka sa ƙasashen duniya suka ɗauki mataki a kan Kosovo, a shekarun 1990. Haka ƙungiyar gamayyar ƙasashen yankin yammacin Afirka wato Ecowas a kan irin waɗannan dalilai na kare hakkin bil addama ta tura wata runduna a soji a yaƙin Laberiya a ƙarƙashin jagorancin Tarrayar Najeriya. A cewar Andres Bock wani masanin kimiyyar siyasa kana malami a jami'ar Ausgbourg da ke nan Jamus, domin tsayar da kisan jama'a kamar yadda ya faru a Kosovo ba tare da miyon bakin MDD. amma ya ce duniya ta rufe ido a kai saboda lamarin ya shafi nahiyar Afirka ne kawai, ya ce amma idan ka duba ai kusan irin abin da ya faru kennan a Kosovo

Ya ce : ''Haƙiƙa a Kosovo a kwai lamari na take hakkokin bil addama abin da ka iya zama hujjar ɗaukar matakin soji a kan ƙasar.''

Yazu yanzu dai babu wani wnda ya san yadda wannan al'amari na ƙasar Siriya zai iya zama game da yadda Rasha da China har ma da Iran suka dage cewar ba su amince ba farmakin da Amirka da kuma sauran ƙasashen duniya ke shirin kai wa Siriya.

Daga ƙasa za a iya sauraron rahoton da wakilinmu na birnin Alƙahira ya aiko mana dangane da a halin da ake ciki a Siriya, sannan a kwai sharhin da Halima Balaraba Abbas ta haɗa mana a kan yiwar ɗaukar matakin soji a kan Siriya. da kuma sharhin da Mohammed Nasir Awal ya rubata mana kan waɗanda ke yin addawa da yunƙurin ƙasashen duniyar a kan Siriyar

Mawallafi : Marcus/Abdourahamane Hassane
Eddita : Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin