Ɗumamar yanayi ya ƙaru a duniya
November 6, 2013Talla
Hukumar ta ce a shekara da ta gabata an sami ƙaruwar yawan iskan mai guba a cikin sararin samaniya a sakamakon dumamar yanayi a duniya. A wani taron manema labarai da yayi a yau domin gabatar da rahoton hukumar na shekara ga 'yan jarida, shugaban hukumar Michel Jarrau ya ce labarin ba shi daɗi ko kaɗan.
Saboda yadda samfarin iskan gaz mai guba da ke gurata muhali iri uku ya ƙaru. Musammum na hayaƙi mai guba wanda ya ƙaru da ƙasa da kishi ɗaya cikin ɗari a shekarun 2011 har zuwa 2012. Hukumar ta ce kishi 60 cikin ɗari na gurɓataccen iskan na gaz da ke bazuwa a cikin sararin samaniya ɗan adam ne dalilin haddasa shi.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman