1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ɓaraka a cikin jam'iyyar APC a Najeriya

October 9, 2013

Wani ɓangaren jam'iyyar ya sanar da haɗewa da jam'iyyar adawa ta PDM.

https://p.dw.com/p/19wtV
Senator Lawali Shuaibu, General secretary ANC party. Foto: DW-Korrespondent Ubale Musa aus Abuja in Nigeria
Lawali ShuaibuHoto: DW/U. Musa

Ɓangaren Rufa'i Hanga na tsohuwar jam'iyyar CPC ya sanar da haɗewa da jam'iyyar adawa ta PDM a dai dai lokacin da jam'iyyar APC ke ƙoƙarin daidaita yadda za ta tinkari yanayin siyasar Najeriyar. Wannan mataki da ɓangaren Sanata Rufa'i Hangan ya ɗauka na bayyana cewar shi da ɗaukacin tawagarsa sun koma jam'iyyar adawa ta PDM ya kawo ƙarshen tsuguni tashin da aka daɗe ana yi a kan makomarsa a jam'iyyar APC, musamman ganin rikita-rikitar da ta faru tsakaninsa da shugabanin tsohuwar jam'iyyar CPC.

Dalilan haɗewar jam'iyyar ta APC da PDM

To sai dai sanin cewar a lokutan baya ya musanta irin wannan yunkuri da aka dangatan shi das hi, duk da cewa ya tabbatar da ana zawarcinsu, ko me ya yi zafi a yanzu da Sanata Rufa'i Hangan ya sanar da haɗewa da jamiyyar ta PDM maimakon jam'iyyar APC?. Ya ce : ‘'Na farako dai CPC ai sun ce ba su yi da mu, kuma an ce mu ba da haɗin kai mun bayar har kira ga jama'a mun yi, amma kuma daga baya muka ga tafiyar nan da wabi, don haka da ni da magoya bayana muka auna muka ga cewa to za mu yi haɗaka da PDM. Domin jam'iyyar APC nan ni ban amince da ita.''

Muhammadu Buhari from the opposition party ANPP (All Nigeria People's Party) acknowledges support after voting in Daura, Nigeria, Saturday, April. 19, 2003. President Olusegun Obasanjo seeks a second term in elections Saturday that pose the stiffest test for Nigeria's young democracy since his election four years ago ended 15 years of military rule. (AP Photo/Schalk Van Zuydam)
Muhammadu BuhariHoto: AP

Martanin jam'iyyar CPC a kan wanan batu

Tun da daɗewa dai tafiya ta yi tsami tsakanin ɓangaren Rufa'i Hangan da na tsohuwar jam'iyyar CPC tun ma kafin a kai ga kafa jam'iyyar APC a Najeriya, to ko yaya ya'yan wannan jam'iyya suke ji da haɗewar da wannan ɓangare ya yi da jam'iyyar PDM da ake wa kalon sabuwa ce a fagen siyasar Najeriyar, wacce hatta tsohon mataimakin shugaban Najeriyar da ake danganata da shi ya daɗe da musanta haka. Injinya Buba Galadani jigo a jam'iyyar APC.

Presidential candidate of Action Congress of Nigeria, Mallam Nuhu Ribadu holds the broom to flag off his presidential campaign rally at the City Centre in Dutse, Jigawa State, on February 28, 2011. Thousands of supporters of the Action Congress of Nigeria waved their brooms, the party's symbol to cheer former Economic and Financial Crime Commission (EFCC) leader and presidential candidate of the party Mallam Nuhu Ribadu, as he began his presidential campaign rally in Dutse, Jigawa State. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Nuhu Ribadu na jam'iyyar ANCHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Ya ce :''Na san Sanata Rufa'i Hanga da shi ne shugaban tsohuwar jam'iyyar CPC na riƙo, kuma yana ƙorafe-ƙorafe yadda ya bar jam'iyyar, idan ya je shi don ƙashin kansa ya shiga wata jam'iyya, mun san dai dama haka zata iya afkuwa. Cewa na ke akwai wanda suke ƙoƙarin shiga jam'iyyar APC ba'a yarda, da su ba har yanzu haƙarasu bata cimma ruwa ba. Na yi imani cewar ko da mutum ɗaya ne aka rasa ƙuri'arsa an yi asara a jam'iyya, amma idan dai wannan ƙuri'ar za ta shigo cikin jam'iyyar don a rinƙa hatsaniya to ai Allah ya raka taki gona.''

Nazarin masu yin sharhi dangane da wannan ƙawance

Koda yake mafi yawan ya'yan jam'iyyar ta APC na hangen ɓangalewar da wannan ɓangare na Rufa\i Hanga ya yi daga tafiya tare da suka faro a jam'iyyar ta APC, ba wani abu ne da zai iya haifara da wani cikas ba, amma masu sharhi a fagen siyasar Najeriyar na ganin rarrubuwar kawauna irin wannan lamari ne da ke iya yin illa ga ƙarfin da jam'iyyun adawa a kan yi ƙoƙarin samu domin tinakrara jam'iyya mai mulki.Malam Abubakar Lado Suleja shi ne shugaban matasa na jam'iyyar ta APC. Ya ce : ''Komawarsu PDM babu wata illa da za ta yi wa jam'iyyar APC domin jam'iyyar APC ta riga ta kafu kuma ta karɓu ga ‘yan Najeriya dama ita suke jira.''

Büro der Oppositionspartei "Actopm Congress of Nigeria" in Abuja, Address No. 16, Bissau Street, Wuse Zone 6, Abuja *** Bild von DW-Mitarbeiter Ubale Musa, 28. Januar 2013
Cibiyar jam'iyyar ACNHoto: DW/U. Musa

Sauya sheƙa ko haɗewar da bangaren Sanata Rufa'i Hangan na jamiyyar APC ya yi zuwa jam'iyyar adawa ta PDM a daidai lokacin da da jam'iyyar APC ke ƙoƙarin ƙara yi wa kanta saiti domin ganin bakin zaren siyasar Najeriyar musamman ma dai tInkrar jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriyar a zaɓuɓɓukan ƙasar da ke tafe a 2015, ya kasance abin da masharhanta ke ganin babban giɓi ne ga wannan jam'iyya.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita : Abdourahamane Hassane

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani