1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar M23 na janye wa daga Goma

November 28, 2012

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce 'yan tawayen sun amince su janye kafin a soma tattaunawa

https://p.dw.com/p/16sAx
M23 rebels patrol around Congo's Central Bank in Goma, eastern Congo, Monday Nov. 26, 2012. Regional leaders meeting in Uganda called for an end to the advance by M23 rebels toward Congo's capital, and also urged the Congolese government to sit down with rebel leaders as residents fled some towns for fear of more fighting between the rebels and army. (AP Photo/Jerome Delay)
Hoto: dapd

Shaidu daga garin na Goma sun ce sun ga motoci da dama na ma'aikatun garin Goma waɗanda yan tawayen suka zara , suna ficewa da garin ɗauke da kayan abinci da kuma makamai,suna garzayawa a garuruwan Rutshuru da Rumangabo da ke a arewacin Goma inda suke da sansani;Omar Fikiira wani ɗan majalisar dokoki ne na arewacin Kiwu kuma ya tabbatar da gaskiyar zance.Ya ce ''har yanzu za a iya ganin motoci na wucewa suna yin saiti wajan Rutshuru inda nan ne cibiyar yan tawayen, ya ce kuma mun yi amanar cewar kamar yadda aka cimma yarjejeniya a Yuganda M23 za ta mutunta.

Shaidun sun tabbatar da ficewar yan tawayen

Daman tun can da farko babban kwamnadan na yan tawayen na M23 janar Sultani Makenga ya gayawa wata kaffa ta ƙasar waje cewar tun a jiya da yamma zasu fara tattara yana su yana su domin ficewa daga Gomar wanda ya ce kafin ranar juma'a sun kammala yin ƙauran baki ɗaya.

Congolese Revolutionary Army (CRA) rebel fighters stand guard as leader of the March 23 Movement (M23) Jean-Marie Runiga arrives in his car to address media in Goma November 27, 2012. Rebels in Democratic Republic of Congo said on Tuesday they would withdraw from the eastern city of Goma if President Joseph Kabila agreed to their demands, which the Congolese government was quick to dismiss as a farce. REUTERS/James Akena (DEMOCRATIC REPUBLIC OF CONGO - Tags: CIVIL UNREST POLITICS MILITARY)
'Yan tawayen ƙungiyar M23Hoto: Reuters

Addadin yan tawayen dai a yanki arewa maso gabashi na Kiwu ya kai dubu ɗaya da ɗari biyar, sannan kamar yadda aka cimma yarjejeniyar a ƙarshen wani taron da ƙungiyar ƙasashen yankin Grand Lac ta gudanar a birni Kampala na Yuganda a makon jiya, ta tanadi cewar dole ne yan tawayen.su janye daga Goma da kilomita 20,dan majalisar ya ci gaba da cewar da alama na ba da daɗewa ba komai zai daidaita.

Ya ce ''ni ina tsamani al'ummar Goma zasu kasance cikin natsuwa da kwanciyar hankali kuma dukanin ma'aikatun zas sake koma aiki ,ya ce na tabbata da zaran yan tawayen sun fice daga Goma ;gwamnatin jihar da majalisar zasu koma aKAn aikin su kamar da.

Yan tawayen na M23 galibi tsohin yan tawayen na ƙabilar tutsit wanda aka saka a cikin rundunar sojojin Kwang akan wata yarjejeniya da aka sa hannu a kai a cikin watan Maris na shekara ta 2009. Sun sake ɗaukar makamai a cikin watan Afrilu na wanan shekara,akan koken da suka gabatar cewar maimakon a watsa su ko'ina a cikin sasa daban daban na ƙasar domin gudanar da aikin soji ya kammata a bar su a yankin su na Kiwu da ke a gabashin domin kare iyalen su.

Al'umma na fuskantar barazana taƙaranci abinci a yanki na Goma

To sai dai kuma daga bisanni jagoran ƙungiyar Jean Marie Runiga ya ɓulo da wasu sabbin sharuɗan cewar tilas ne a gudanar da bincike akan wani yunƙurin kisa da aka so yi; akan wani ƙwarraran likitan Mukwege Denis; wanda ya yi sunna wajan ba da tallafi ga matan da aka yiwa feyɗe tare da ba da yancin yin walwala ga jagoran yan adawa Etienne Tshisekedi da kuma rusa hukumar zaɓe.Yanzu haka dai mutane kusan dubu ɗari biyar ne suka yi ƙaura daga garin Goma sakamakon tashin hankali, kana kuma matsalar ruwan sha na fomfi da wutar lantarki da magunguna da kuma abinci na iya ƙara dagulewa nan gaba, idan har al'amura basu daidaita ba saboda yawancin abinci da ake kai ;wa a sauran yankunan ƙasar ana fitar da shi ne daga Goma.

Congolese flee the eastern Congolese town of Sake , 27kms west of Goma, Friday Nov. 23 2012. Thousands fled the M23 controlled town as platoons of rebels were making their way across the hills from Sake to the next major town of Minova, where the Congolese army was believed to be regrouping. The militants seeking to overthrow the government vowed to push forward despite mounting international pressure.(Foto:Jerome Delay/AP/dapd)
Jama'a na yin ƙaura daga yankin arewa maso gabashin Kwango saboda yaƙiHoto: AP

Hukumomin Kwango na zargin Ruwanda da Yuganda da tallafa wa 'yan tawayen

Ƙasar dai ta Kwango daman ta yi fama yaƙin basasa har so biyu a can baya a shekarun 1996 zuwa 1997 da kuma shekarun 1998 zuwa 2003 wanda ƙasar ta riƙa samun tallafi daga Angola a fadan da ta gwabza da ƙungiyoyin yan tawayen da ke samun goyon bayan Ruwanda da Yuganda da Burundi,a yanzu kuma Kwango da MDD na zargin Ruwanda da Yuganda da mara wa yan tawayen na ƙungiyar M23 baya.

Rwandan President Paul Kagame (L), his counterparts Yoweri Museveni (C) of Uganda and Joseph Kabila (R) of the Democratic Republic of Congo's (DRC) attend on November 21, 2012 a summit meeting at the Speke Resort in the Kampala suburb of Munyonyo. The leaders of the Democratic Republic of Congo, Rwanda and Uganda said on November 21 that the M23 rebels who have seized the eastern Congolese town of Goma must pull out immediately. The United Nations accuses Rwanda of backing M23 fighters who now control Goma, charges Kigali denies. Uganda has also dismissed charges it has aided the rebels. AFP PHOTO / PETER BUSOMOKE (Photo credit should read PETER BUSOMOKE/AFP/Getty Images)
Kagame da Museveni tare da Kabila a GomaHoto: Peter Busomoke/AFP/Getty Images

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi

Daga ƙasa za a iya sauraron wanan rahoto