Ƙoƙarin Uganda na bunƙasa noma ta amfani da takin gargajiya
Noman gargajiya wa masu matsakaicin ƙarfi
Timatirin da aka noma da takin gargajiya, ba kama ido kaɗai ya ke da shi ba - ya kan kawo wa manomi kuɗi. Yanzu ba a ƙasashen ƙetare kaɗai irin wannan amfanin gonan ke tsada ba, ko a Uganda mutane kan saye shi da farashi mai tsada. Masu matsakaicin ƙarfi na samun kuɗi sosai a Uganda
Ɗanyen kayayyakin abinci daga an yi oda
Da "Boda-Boda" abun da ake kiran babur a Uganda, manoman ke kai amfanin gonan nasu zuwa shagunan kayayyakin a babban birnin ƙasar wato Kampala, inda 'yan kasuwan ke jira da odan da mutane su ka tura, ana saukewa za'a tura musu tun kafin wani abu ya same su.
Samun takardar shaida na irin wannan noman na da tsada
"Nogamu", Ƙungiyar manoman gargajiyar ta Uganda, ta kan baiwa manoma irin su Vincent Ssonko shawarwari kan dabarun noma da hanyoyin samun takardar shaida. Mutane milliyan 1, 2 ke ƙungiyar, cikinsu 200,000 kaɗai ke da takardar izinin yin wannan noman, domin kaɗan daga cikinsu kaɗai zasu iya biyan kuɗin da ake buƙata
Matakan tabbatar da sahihanci kayayyaki masu tsauri
A kusa da shagunan kayayyakin gonan na gargajiya da ke Kampala, akwai shagunan 'ya 'yan itace da na kayayyakin lambu da ba su ƙetare mizanin kasancewa a wannan rukunnin ba. Yawancin manoma a Afirka na gaza yin wannan noma saboda tsadan magungunan ƙwari, amma sukan sami irin da aka samu ta wannan salon noman ko kuma su yi amfani da takin gargajiya kaɗai
Buƙatun ƙasashen ƙetare
Jamus na shigo da abarbar Uganda mai zaƙi kamar suga. Lokacin baje - kolin kayayyakin da aka noma da takin gargajiya a Nürenberg a watan Fabrairun 2013, wakilai 13 suka zo daga Uganda. Ko da shi ke maƙotan Ugandan ma kamar Kenya da Sudan suma su kan shigar da ta su abarbar, kuma jama'a kan saye su da tsada fiye da wanda aka noma ta hanyar da aka saba
Ɗanɗanon kayayyaki, noman gargajiya ya fi na wanda aka saba
Mata da dama a Uganda na samun kuɗi daga cinikin 'ya'yan itace da kayayyakin lambu. Waɗannan mata, sun yi shekaru suna sayar da ayaba shukan gargajiya. Masu saye suna sha'awan ɗanɗanon shi ko a lokacin da bai gama ƙosawa ba. Saboda wannan sukan yi tafiya mai nisa da babur domin samun kayayyakin
Ƙarin kuɗin ɓatarwa a asusun gida
Masu noman gargajiya na samun kyakyawan girbi, kuma suna samun kuɗi, wanda ya ke rage nauyin samar da abubuwan more rayuwa, amma kuma a waje guda akwai muhalli wanda ke tasiri, musamman ma a Afirka, inda akwai matsalolin da ke da nasaba da sauyin yanayi.
Gahawa ce aka fi aikawa ƙasashen ƙetare
Gahawan Uganda, ta yi suna a ciki da wajen ƙasashen ƙetare, haka ma Jamus, wadda ta kasance ƙasar da ta fi amfani da gahawar a duk faɗin duniya na ɗaya daga cikin masu shigar da ita. Ƙasar noman Uganda na da kyau sosai kuma ta na da nauo'in da gahawar ke buƙata.
Kama da wane bata wane
Wannan gahawar da ta tsuro da kanta ne a wani fili da ke yankin arewa maso yammacin Uganda. Wannan ba ta samu irin kulawar da ake so ba, saboda haka zata banbanta da shukan gargajiya, tunda ba'a yi tattalin ƙasar yadda ya kamata kafin a shuka irin ba
Gahawa mai suna "Bio Arabica" ɗari bisa ɗari
A yankin arewa maso yammacin Uganda, akwai manoman da ke da izinin noman gahawar, bayan an yi girbi, akan shanya waken gahawar a rana ya bushe kafin a gyara shi. Daga ƙarshe sai ai kai shi shago a babban birnin ƙasar ko kuma nan Jamus inda akwai masu son amfani da shi