Ƙaruwar ayyukan Alƙa'ida a Yamen
August 6, 2013A ƙasar Yamen 'yan bindga sun kakkaɓo wani jirgin mai saukar ungulu wato na sojin, inda dukkan sojoji takwas da ke ciki suka mutu, ciki harda wani kwamandan sojojin. Rahotanni suka ce an kakkaɓo jirgin a yankin Wadi Ubida, inda ƙungiyar Alƙa'ida ta fi ƙarfi. Wannan harin ya zo ne a dai-dai lokacin da ƙasashen yamma ke nuna shakku a kan Yamen, tun bayan gargaɗin da Amirka ta yi na yiwuwar kai harin ta'addanci. Ƙasar Amirka dai ta fara ƙwace wasu daga ma'aikatanta daga birnin Sana'a babban birnin ƙasar ta Yamen. Rundunar mayaƙan saman Amirka ce ta fitar da ma'aikatan waɗanda ke aiki a ofishin jakadancin Amirka. Wannan kuwa shi ne matakin baya-bayan nan da ƙasar ta Amirka ta ɗauka, dangane da sanarwar da ta yi na rufe ofisoshin jakadancinta a wasu ƙasashen musulmi, a wani abin da ta ce wai ta samu bayyanai da ke nuna cewa ƙungiyar Alƙa'ida na shirin kai wa ƙasashen yamma harin ta'addanci.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita. Abdourrahmane Hassane
AP