1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana fama da karancin abinci a Kamaru

Zakari Sadou
December 18, 2023

Al'ummar Kamaru kimanin miliyan uku na fama da karancin abinci tun 2021 sakamakon matsalolin tsaro da sauyin yanayi da kuma ambaliyar ruwa a wasu yankunan kasar.

https://p.dw.com/p/4aJNI
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Kashi 11% na al'ummar Kamaru na fama da karancin abinci, wato kusan mutane miliyan uku kamar yadda alkaluman da hukumar samar da abinci ta duniya WFP ta gabatar wa gwamnatin kasar suka nunar. Gwamnatin dai ta baiyana shirinta na shawo kan lamarin.

Ministan noma da raya karkara Gabriel Bairobe ya damu matuka da yawan mutanen da suke fama da karancin abinci a kasar. Ya ce ya kamata a dauki matakan gaggawa na magance matsalar 

 Matsalar karancin abinci a Kamaru ta fara ne tun 2021 a lokacin cutar COVID-19 ga kuma rikicin Ukraine da Rasha lamarin da ya kara hauhawar farashin kayan abinci musamman alkama da shinkafa, a bangare guda kuma ga matsalar ambaliyar ruwa a arewacin Kamaru mai nisa wacce ke da alaka da dumamar yanayi, uwa uba kuma rikicin sashin renon Inglishi, ga kuma hare haren kungiyar Boko Haram wanda ya tilasta wa miliyoyin al'ummar yankunan tsarewa daga matsugunansu.

Gwamnatin Kamaru ta dora alhakin karin kashi 15 zuwa 30 cikin 100 na farashin kayan abinci, musamman Alkama, Marasa, Dawa da kuma Shinkafa da aka fi amfani da su a yankunan da ke kan iyaka da Najeriya da Chadi.

 Kasar Kamaru ta dogara da Ukraine da Rasha wajen shigo da kashi 60 cikin 100 alkama.