1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Kamaru ta kauce wa daukar matsaya

Lateefa Mustapha Ja'afar ZUD
August 1, 2022

Ko Kamaru ta yi tir da mamayar Rasha a Ukraine? Shugaba Paul Biya bai amsa tambayar da 'yar jaridar Faransa ta yi masa ba. Biya ya ce bai fahimta ba, har sai da shugaban Faransa da ke kusa da shi ya maimaita masa.

https://p.dw.com/p/4Es5K
Emmanuel Macron in Kamerun
Hoto: Stephane Lemouton/abaca/picture alliance

Jaridar Die Tageszeitung a sharhinta mai taken: Sansanin Majalisar Dinkin Duniya a Kwango, ya zama tamkar mayanka. Ta ce: Mutane da dama sun halaka a kokarin murkushe zanga-zangar nuna adawa da kasancewar Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da karfin tuwo. Jaridar ta ce zanga-zangar nuna kin jinin rundunar MONUSCO a Kwangon da ta rikide zuwa tashin hankali, ita ce mafi muni a tarihin shirin wanzar da zaman lafiya na majalisar. Abin da ya sanya dimuwa da kuma tambayar shin ko akwai bukatar ci gaba da kasancewar su a wannan babbar kasa?

Zanga-zangar ta haifar da fasa shaguna da sace-sace a Goma, babban birnin gundumar arewacin Kivu da ke fama da rikici, kafin daga bisani ta yadu zuwa birnin da ke makwabtaka wato kudancin Kivu. Rahotanni sun nunar da cewa kwana guda bayan fara zanga-zangar, mutane 15 sun halaka yayin da aka harbe fararen hula hudu har lahira. Tun dai bayan yakin basasar da aka yi a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon tsakanin shekarun 1998 zuwa 2003 ne, Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniyar ta MONUSCO ke kasar. 

Außenministerin Baerbock besucht Mali
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock da sojojin Jamus da ke MaliHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Rundunar sojojin Jamus ta Bundeswehr ta makale

Jaridar Neues Deutschland ta ce rashin jituwa tsakanin gwamnatin kasar Mali da Majalisar Dinkin Duniya, ka iya kawo karshen shirin wanzar da zaman lafiya na majalisar a Mali cikin sauri. Yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine, ya sanya ana mantawa da sauran yankuna da ke fama da rikici a duniya. Rikicin kasar Mali, inda rundunar sojojin Jamus ta Bundeswehr ke da sojoji masu tarin yawa a shirinta na tsaro a kasashen ketare, na daga cikin rikicin da ke fama da rashin tabbas. Jaridar ta ce Masu jihadi a yankunan Mopti da Koulikoro, na kara nuna cewa za su iya kai munanan hare-hare duk kuwa da farmakin da sojojin Malin ke kai musu. Tsawon kwanaki biyu suka kwashe suna kokarin kwace sansanonin sojojin Mali mafiya girma a Kati, mai nisan kilo mita 15 da Bamako fadar mulkin shugaban mulkin sojan kasar ta Mali Kanal Assimi Goïta.

Kafin harin na Kati, mahara sun kai hari a sansanin soja na Zantiguila. Kungiyar 'yan ta'addan Katiba Macina da ke arewcin Mali ce ta dauki nauyin harin, kuma a yanzu tana kokarin isa fadar gwamnati. Babu tabbas ko sojoji da jami'an tsaron Malin da kuma taimakon sojojin haya na Rasha ka iya dakatar da su. Tun tsawon sama da shekaru 10 ne dai, 'yan ta'adda suka addabi kasar ta Mali. Hakan ta haddasa samar da Rundunar Wanzarn da Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Malin wato MINUSMA a shekara ta 2013 domin yaki da 'yan ta'addan.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov da mataimakin firaministan Habasha Demeke Mekonnen Hassen
Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov da mataimakin firaministan Habasha Demeke Mekonnen HassenHoto: Russian Foreign Ministry Press Service/AP/picture alliance

Rasha na zawarcin Afirka kan yakin Ukraine

Jaridar Süddeutsche Zeitung a sharhinta mai taken: Komawa lokacin yakin cacar-baka, ministan harkokin  wajen kasar Rasha Sergey Lavrov na zawarcin kasashen Afirka. Jaridar ta ce babu tabbas ko ministan harkokin kasashen ketare na Rasha Lavrov ya yi niyyar zuwa yankin Oyo da ke arewacin Kwango. Yankin da ke da yawan al'umma 500,000, ana damawa da shi a siyasar duniya. Lavrov ya kuma ziyarci Masar da Yuganda da kuma kasar Habasha, cibiyar kungiyar Tarayyar Afirka, AU. Cikin kwanaki biyar, ya kammala ziyarar kasashen hudu, inda ya yaba da matsayar Afirka kan yakin da Rashan ke yi da Ukraine. Duk da cewa kasashen nahiyar Afirka 54 ba sa magana da murya guda, amma Rasha na da tabbacin kasancewar wasu 'yan ba ruwanmu yayin da wasu kuma suka kasance masu taka-tsan-tsan.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Benin Shugaba Patrice Talon
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Benin Shugaba Patrice TalonHoto: Ludovic Marin/AFP

Macron ya ziyarci kasashen da Faransa ta mulka

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cikin sharhinta mai taken: Macron ya koma kasashen da Faransa ta mulka. A yayin ziyararsa a Afirka, shugaban kasar Faransa ya shaida tasirin farfagandar Rasha. Jaridar ta ce: Ko Kamaru ta yi tir da mamayar Rasha a Ukraine? Mai shekaru 89 a duniya, Shugaba Paul Biya bai amsa wannan tambayar da 'yar jaridar Faransa ta yi masa ba a yayin taron manema labarai da takwaransa na Faransan Emmanuel Macron. Biya ya ce mata bai fahimci abin da take tambaya ba, 'yar jaridar ta sake tambaya amma duk da haka ya ce bai fahimta ba har sai da Shugaba Macron da ke kusa da shi ya maimaita masa. Ziyarar ta Macron ta farko tun bayan sake zabarsa a wa'adi na biyu, na zaman ta kokarin tunkarar tasirin Rasha a kasashen da Faransan ta raina kuma ta zo ne a daidai lokacin da ministan harkokin kasashen ketare na Rasha Sergey Lavrov ke ziyara a Afirkan. Kasashen Afirka 25 dai, sun ki sukar Rasha yayin kada kuri'ar yin tir da kaddamar da yaki a Ukraine da Moscow ta yi a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya. Macron dai na kokarin farfado da kimar Faransa a idanun Afirka musamman kasashe rainonta. Bayan Kamaru Macron ya kuma ziyarci kasashen Benin da Guinea-Bissau.