Sa-In-Sa tsakanin gwamnati da kungiyoyin Nijar
March 29, 2018Talla
A Jamhuriyar Nijar alaka na ci gaba da tsami tsakanin mahukunta da kungiyoyin fararen hula a jamhuriyar Nijar, bayan turjiya da nuna kyama da masu fafutikar ke yi da tsarin kasasfin kudin kasar na bana.
Masu gwagwarmayar a wani yankurin, sun yi zanga-zangar da ta kai ga kame jagorinsu bayan haramta harkokinsu da hukumomi suka yi. Hakan ya kuma tayar da wata sabuwar takaddama a kasar, inda ake ci gaba da tsare shugabannin kungiyoyin a ofishin jami'an 'yan sanda cikin kwanakin da suka gabata.
Baya ma ga tsare wasunsu da 'yan sanda suka yi, an ma kaiga gabatar da su gaban kuliya bayan tsanantar turjiyar a fadin kasar.