1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kotu ta daure jagororin farar hula

Abdul-raheem Hassan
March 27, 2018

Mutane 23 ne 'yan sanda suka tsare bayan barkewar hatsaniya a yayin gudanar da zanga-zangar adawa da sabon tsarin kasafin kudin kasar, kotun ta tura mutane biyar gidajen yari daba-daban da ke fadin kasar.

https://p.dw.com/p/2v5gB
Niger Niamey Opposition
Hoto: DW/M. Kanta

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta bukaci hukumomin Nijar su saki jagororin gwagwarmayar da ke tsare, a cewar kungiyar, ci gaba da tsare su zai haddasa sabuwar rigima tsakanin fararen hula da jami'an tsaro.

Sai dai ministan harkokin wajen kasar Bazoum Mohammed ya ce kamen na kan ka'ida, ganin yadda aka haramta zanga-zangar saboda dalilai na tsaro.

Nijar dai na cikin kasashen yammacin Afirka da ke yawaitar fuskantar zanga-zanga, sai dai a Nijar din kungiyoyin farar hula na sa in sa da gwamnati kan sabbin tsare-tsaren da suka shafi karin harajin wayar salula.