Rikici tsakanin makiyaya da manoma ya ki ci ya ki cinyewa
April 28, 2016Talla
Rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma na cigaba da janyo asarar rayuka da dukiyoyi musamman a tarayyar Najeriya duk kuwa da matakan da mahukunta da ma kungiyoyi masu zaman kansu ke yi na kawo karshen sa. Sai dai duk haka ba a yi kasa a guiwa ba wajen gano mafita daga rikicin na tsawon shekaru.