Rikicin kabilanci ya barke a Adamawa
January 24, 2016Ana dai zargin cewar fulani makiyaya ne suka afkawa yankin, a wani abin da aka ce hari ne na fansa, bayan wata rigima da ta shiga tsakanin al'umomin biyu a kwanakin baya.
Wani maharbi mai suna Aliyu Kaura, ya shaidawa wakilinmu na Yola Muntaqa Ahiwa cewar lamarin ya kazanta saboda ya kai ga kone-konen gidaje da dama.
a inda ya kara da cewar dama a kwai wata jikakkiya a kwance a tsakanin kabilun biyu kana kuma a kwai yuwuwar cewar an kashe D.P.O a yankin da yaje kokarin saisaita rigimar.
Rikicin wanda ya barke tun a ranar a sabar da tsakar dare ya lakume rayukan mutane da dama sai dai ya zuwa yanzu babu wasu cikakkun bayanan binciken karin bayani daga jami'an tsaro a karamar hukumar Girei a cikin jihar ta Adamawa a Najeriya.