1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta dakatar da Nijar daga kungiyar

Binta Aliyu Zurmi
August 22, 2023

Kungiyar tarayyar Afirka AU ta dakatar da jamhuriyar Nijar daga duk wasu ayyukan kungiyar har sai kasar ta koma a kan mulkin dimukuradiyya.

https://p.dw.com/p/4VRw7
Moussa Faki Mahamat | AU
Shugaban hukumar AU, Moussa Faki MahamaHoto: Simon Maina/AFP

AU ta umurci sojojin da ke rike da madafun iko da su mayar da hambararen shugaban kasar Mohamed Bazoum kan mulki tare da komawa barikinsu.

Kwamitin sulhu na AU ya goyi bayan matakin da kungiyar ECOWAS ta dauka na girka rundunar ko-ta-kwana don daukar matakin soji idan sulhu.

Kazalika AU ta yi kira ga duk mambobinta da ma kasashen ketare da su kauce wa halasta ayyukan sojojin Nijar, kuma da babbar murya ta yi kira ga kasashen da ba na Afirka ba cewar ba ta son wani katsalandan daga garesu.

A watan jiya ne dai sojojin Nijar suka hambarar da gwamnatin farar hula tare kuma da ci gaba da tsare Shugaba Mohamed Bazoum.