1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar ECOWAS ta sake komawa Nijar

August 19, 2023

Wata tawagar wakilan kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta isa birnin Yammai domin duba yiwuwar sake tattaunawa da sojojin da suka hambarar da mulkin shugaba Mohamed Bazoum.

https://p.dw.com/p/4VM2D
Hoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun yi nuni da cewa, wata tawaga ta kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta isa birnin Yammai domin tattaunawa da sojojin da suka hambarar da mulkin shugaba Mohamed Bazoum da nufin kawo karshen dambarwar juyin mulkin kasar ta hanyar sulhu.

Hakan dai na zuwa ne kwana guda bayan da manyan hafsoshin sojin kungiyar suka kammala wani zama na kwanaki biyu domin lalubo hanyar ci gaba da matsa wa jagororin juyin mulki lamba su mika mulki ga gwamnatin farar hula.