1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

An tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan Gaza a Turkiyya

November 6, 2023

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito cewa 'yan sandan sun tarwatsa masu zanga-zangar lumanar da ruwan zafi, bayan da suka fara tunkarar sansanin sojin Amurkan

https://p.dw.com/p/4YQhI
Hoto: Adem Altan/AFP/Getty Images

'Yan sandan kasar Turkiyya sun tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kusa da sansanin sojin Amurka da ke Ankara babban birni kasar, sa'o'i kalilan kafin saukar sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a kasar don fara ziyarar aiki a yau, inda zai gana da ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan a gobe litinin.

Karin bayanAsibitoci da dama sun rufe a Zirin Gazai:

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito cewa 'yan sandan sun tarwatsa masu zanga-zangar lumanar da ruwan zafi, bayan da suka fara tunkarar sansanin sojin Amurkan, ko da ya ke babu rahoton kama kowa ko kuma jin rauni daga masu zanga-zangar.

A gefe guda kuma a yau din dai mutane kusan dubu guda sun gudanar da wata zanga-zanga a bakin harabar ofishin jakadancin Amurka da ke birnin na Ankara.

Karin bayani:Guterres ya bayyana damuwa kan kisan mutane a Gaza

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sha fitowa fili karara yana nuna goyon bayansa ga Falasdinawa.