1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙoƙarin sanya ilimin addini cikin na zamani

April 10, 2012

Shugaba Jonathan na Najeriya ya kaddamar da makarantar kwana ta zamani a Sokoto da za ta koyar da Almajirai ilmin zamani da na addini a haɗe, don magance bara.

https://p.dw.com/p/14aWC
Nigeria Koranschule Schüler Schüler in weißen Gewänder sitzen auf dem Fußboden im Klassenraum in einer neuer/moderner Koranschule in Sokoto, Nigeria Wer hat das Bild gemacht?: Aminu Abdullahi Abubakar (DW Korrespondent) Wann wurde das Bild gemacht?: 10.04.2012 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Sokoto / Nigeria
Hoto: DW

Yara Almajirai sama da miliyan 9 ne aka kiyasta ake da su a Najeriya, wanda dukkan su ke gudanar da barace-barace da sunan neman ilmin addini ba tare da samun damar neman ilmin zamani ba.

Hakama yawan almajiran a yankin arewa ya sa hukumomi ke zargin a nan ne ake samun Matasa na tashi da aƙidar tsatsaurar ra'ayi na addini da ke kai Matasa shiga kungiyoyin taaddanci saboda rashin samun kulawa da tarbiyar su da akeyi.

Shugaba Goodluck ya kaddamar da makarantar kwana ta almajirai da gwamnatin sa ta gina a sokoto a cikin 400 da za'a gina a fadin arewa.

“Yace wani bincike da kwaminitin kula da ilmin almajirai ya gudanar a shekarar 2010 ya nuna cewa, akwai Almajirai sama da miliyan 9 a najeriya kuma a cikin su Yankin arewa maso yamma kadai nada almajirai miliyan 5 da rabi wato kashi 60 a cikin dari na almajirai da ake dasu a kasa baki daya.”

Nigeria Koranschule Schüler Schüler in weißen Gewänder sitzen auf dem Fußboden im Klassenraum in einer neuer/moderner Koranschule in Sokoto, Nigeria Wer hat das Bild gemacht?: Aminu Abdullahi Abubakar (DW Korrespondent) Wann wurde das Bild gemacht?: 10.04.2012 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Sokoto / Nigeria
Hoto: DW

Don haka shugaban ya ce dole ne a dauki matakai na ganin kowane almajiri ya samu kula ta ilmi kamar yadda yaro dan kasa ke samu.

Mai martaba sarkin musulmi daya bada fili da aka gina makarantar yace hakkin kowane dan kasa ne don ceto rayuwar yaran mu a fanin basu ilmi na addini da zamani.

“ Neman ilmi hakki ne ga kowane musulmi ko musulma, don haka a nasu bangare na shugabannin addini da alumma dole su tashi tsaye su ga bayan yawon almajirci, a kan haka a bada tabbacin goyon banan su ga samun nasarin wannna shirin na ilmantar da almajirai ilmin addini da zamani a hade”

Ƙoƙarin gwamnatin Sokoto

Tuni dai gwamnati jihar Sokoto a karkashin Alh Aliyu Magatakarda ta ƙirƙiro irin wannan makaranta don magance matsalar barace-barace na almajirai

“ Mun kafa irin wannna makarantar ta almajirai a garin shuni mai kula da almajirai dari 800 don ganin an hade ilmin zamani da na addini a waje daya ga almajiran”

Unterricht in einer Schule im Dorf Tibiri nahe Maradi im Süden des Niger, aufgenommen am 05.11.2007. Die Schule gehört zum "Haus der Hoffnung" und wurde von einer luxemburgischen NGO (Non-Governmental Organization) gegründet, um Kindern zu helfen, die durch die Folgen von mit Fluor kontaminiertem Trinkwasser aus einem Brunnen in der Nähe erkrankt sind. Besonders in den ländlichen Gebieten des westafrikanischen Landes stellt die Beschaffung von sauberem Trinkwasser ein großes Problem dar, nur rund 30 Prozent der Bevölkerung haben Zugang dazu. Die Möglichkeit eine Grundschule zu besuchen haben nur rund 40 Prozent der Mädchen und 60 Prozent der Jungen. Der südlich der Wüste Sahara in der Sahelzone gelegene Niger gehört zu den ärmsten Ländern der Welt.
Hoto: picture alliance / ZB

Wasu malaman zaure da ke karantar almajiran da basu yarda na dauki muryar su, sun bayyana shirin bude makarantar da cewa siyasa ce kuma yan kwanakki zaa ga yaran sun dawo yawon almajirci, sai hakan yasa Malam Lawal Maidoki na Kungiyar Nocomyo ya ki amince da wannan zargin.

Iyayen kasa da matsalar almjirci ke ciwa turo a kwarya suna gudanar da kira ga iyayen yara almajirai dasu rungumu shirn tsarin ilmi don saka ya'yansu a cikin ilmin zamani, kamar yadda Alh. Bello Abubakar Ubandawakin Maberar jariri ke shedar.

Gwamnatin tarayyar Najeriyar dai zata kashe kudi naira biliyan 5 don gina makarantun ilmin almajirai 400 a dukkan johohin arewa 19 don kawo karshen yawo bundi da yara keyi daa sunna neman ilmi na addini.

Mawallafi: Aminu Abdullahi Abubakar

Edita : Zainab Mohammed Abubakar