Zuma ya sauka daga shugabancin ANC | Labarai | DW | 16.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zuma ya sauka daga shugabancin ANC

Shugaba Zuma na Afirka ta Kudu ya sauka daga shugabancin jam'iyyarsa ta ANC bayan shekaru 10 na jagorancinta. A wannan Lahadi jam'iyyar za ta zabi sabon jagoranta.

Da yake jawabi a gaban dubunnan magoya bayan jam'iyyar ta ANC a wurin wannan taro, Shugaba Jacob Zuma ya tabbatar da komabayan da jam'iyyar ta fuskanta a shekaru 10 na jagorancinsa.

Ya ce al'ummar kasar ba ta gamsu da jam'iyyar da ke mulkin ba musamman kan batun cin hanci da rashin aikin yi da kuma miyagun ayyuka da suka karu a cikin shekaru 10 na mulkinsa. 

Shugaba Zuma ya bayyana rashin nasarar jam'iyyar ta ANC da yadda su 'ya'yanta suka mayar da hankali ga cin junansu  a maimakon tunkarar kalubalen da ke a gaban kasar. A wannan Lahadi ce dai jam'iyyar ta ANC za ta zabi sabon shugabanta.