Zubar dusa ƙanƙara a Amirka na dagula al′amura | Labarai | DW | 03.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zubar dusa ƙanƙara a Amirka na dagula al'amura

Hukumomi a Amirka sun soke tashin jiragen sama kusan dubu uku sakamakon zubar dusar ƙanƙara a yankin arewa maso gabashi na ƙasar.

Hukumomin su yi gargaɗin cewar jihohin New York da New Jersy da Boston da sauransu zasu kasance waɗanda lamarin zai fi shafa.

A jihar Massachusetts inda ƙanƙarar ke zuba da ƙarfi tun jiya gwamnan jihar ya ba da umurnin rufe makarantu sannan kuma ya gargaɗi jama'a. Ya ce : '' Ana cikin wani yanayin sanhi ƙanƙara mai muni wanda zai ci gaba har yau da zuwa gobemuna gargaɗar jama'a da su tsaya a gidajensu, tare da ɗaukar matakai na kariya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman