1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Macron ya ziyarci Tarayyar Najeriya

Salissou Boukari
July 3, 2018

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sauka a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya, inda ya gana da takwaransa na Najeriyar Muhammadu Buhari a kokarin da yake na kara karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/30lhF
Burkina Faso Besuch Emmauel Macron Universität in Ouagadougou
Hoto: Reuters/P. Wojazer

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya sauka a wannan Talatar a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya, inda ya gana da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari a kokarin kara karfafa dangantakar da ke tsakanin kasarsa ta Faransa da kasashen Afirka renon Ingila inda a bara ma ya ziyarci kasar Ghana.

Jirgin Macron ya sauka ne a Abuja bayan da ya taso daga kasar Mauritaniya inda shugaban ya halarci babban taron koli kungiyar Tarayyar Afirka karo na 31, wanda ya mayar da hankali kan batutuwan tsaro a yankin Sahel mai fama da tashe-tashen hankulla na 'yan ta'adda.

Tsohon ma'aikacin banki, shugaban na Faransa ya taba zama na tsawon watanni shida na koyon aiki a ofishin jakadancin Faransa da ke Abuja lokacin yana dan makarantar koyon aikin hukuma a wajejen shekara ta 2000, inda ya shaidawa 'yan jaridar da suke hira cewa yana mai son Najeriya domin kasa ce mai kwarjini, ta haka ne ma tun bayan hawansa mulki, Macron ya nemi karfafa huldar kasarsa da Tarayyar ta Najeriya.

Bayan tattaunawa da shugaban Najeriya Macron zai bar Abuja zuwa birnin Lagos inda zai karfafa ziyarar ta shi kan abubuwan da suka shafi al'adu a birnin Legas.