1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ziyarar Shugaban gwanatin Jamus Gehard Schroder a Bosnia da Turkiyya

Zainab A MohammedMay 3, 2005

Shugaban gwamnatin jamus na rangadin aiki na yini biyu a Turkiyya

https://p.dw.com/p/BvcA
Hoto: AP

MOD.:Shugaban Gwamnatin Jamus gehard Schroderya yabawa yadda lamura na siyasa da tattali ke ingantuwa a Bosnia,wanda zai bata daman inganta hulda da kasashen turai.

Shugaba Gehard Shroderwanda yayi wannan yabon a yayin ziyaran yini guda daya kai a Bosnia,yakuma yi fatan cewa kungiyar gudanar da turan zatayi maraba da wannan cigaba da aka samu a wannan kasa domin cimma yarjejeniya daidaituwa,wanda ke zama mataki na farko na neman amincewa da ita cikin kungiyar ta gamayyar turai.

Bosnia kadai ta rage kasa dake yankin Balkan wadda har yanzu bata cimma wata nasaran wata hulda na kut da kut da kungiyar ta EU ba duk da kiran da hukumar gudanar da kungiyar tayi wa kasashen yankin a watan Afrilu.

A ranar 19 ga wannan wata ne hukumar zatayi nazari kan irin nasarori da Bosnia ta cimma wajen gyare gyare,a matsayin sharan fage.

Shugaba Schroder yace Bosnia ta cimma nasarori da dama wajen gyaran bangaren sharianta da harkoki na gudanar da gwamnati,cikin shekaru 2 da suka gabata,kana ya yabawa yunkurin da tayi ta fanning gyaran sashin tsaron kasar ,wanda kuma ke zama daya daga cikin abubuwa biyu da zai share fagen fara tattauna batun gamewa da kungiyar tarayyar turai.

Bugu da kari ana bukatar Bosnia ta bada cikakken hadin kanta wa kotun hukunta masu laifin yaki ta mdd dake birnin Hague,inda nan ma shugaban gwamnatin na jamus ya yabawa Bosnia,dangane da mikawa wannan kotu sabiyawa 9 dake da laifukan yaki akansu a farkon wannan shekara.

A dangane da hakane a hiran da yayi da manema labaru tare da shugaban Bosnian Shugaba Schroder ya jaddada bukatar cigaban wadannan nasarori da aka samu.

A nashi bangare Prime minister Adnan Terzic na Bosnia,yayi maraba da wannan ziyara na shugaban gwamnatin Jamus a karo na farko,tun bayan yakin daya gudana daga 1992.5,kana ya bada tabbacin cewa Bosnia zata taka muhimmiyar rawa gain wajen tabbatar da ingantaccen tsaro a wannan yankin baki daya.

Ya kara dacewa wannan shine babban goyon baya da kasarsa ta samu,wanda zai kara mata kwarin gwiwa dangane da sauran gyare gyarenta.

Alokacin wannan ziyara tasa Shugaban gwamnatin na jamus ya gana da kungiyar mata daga Srebrenica,inda Sabiyawan Bosnia sukayiwa muslimi kimanin 8,000 yankan rago,inda yayi musu alkawarin tallafin tsaro a wannan yanki daya kasance abun razana.

Acigaba da ziyarar tasa ta yini biyu shugaba Gehard Schroder a yanzu haka ya sauka a birnin Ankaran kasar Turkiyya,inda zai gana da prime minister Tayyip Erdogan.Tattaunawan nasu dai bazai kasa nasaba sa yunkurin turkiyya na hadewa da kungiyar tarayyar turai ba.Shugaban na Jamus dai na daya daga cikin magoya bayan hadewar Turkiyyan anan nahiyar turai.