1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaba Hu Jintao na kasar Sin a nan Jamus

YAHAYA AHMEDNovember 10, 2005

A ziyarar kwana 3 da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya kawo wa Jamus tun daga yau alhamis, zai yi shawarwari da shugabannin gwamnatin tarayya, inda kuma zai gana da shugaban gwamnati mai barin gado, Gerhard Schröder da Angela Merkel, wadda za ta kasance sabuwar shugaban gwamnatin nan ba da daewa ba. Daya daga cikin muhimman batutuwan da shugaban Sin din zai tattauna a nan Jamus, shi ne batun dage takunkumin sayad da makamai da Kungiyar Hadin Kan Turai ta sanya wa kasarsa.

https://p.dw.com/p/Bu4K
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin.
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin.Hoto: AP

A lokacin da mataimakan shugaba Hu Jintao na Sin ke tsara masa shirye-shryen ziyarar da zai kai a kasashen Turai, sun yi zaton cewa idan ya iso nan Jamus, zai sadu ne da sabuwar gwamnati. Amma a daidai lokacin ziyararsa a birnin Berlin, wadda zai fara yau, jam’iyyun CDU da SPD na nan na ta tattaunawa kan kafa gwamnatin gambiza. Har ila yau dai, ba a rantsad da gwamnatin tarayya ba tukuna. Shi ya sa shugaba mai barin gado, Gerhard Schröder, shi ne zai fara musayar yawu da babban bakon daga Sin, Hu Jintao. Kafin barinsa Jamus jibi dai, shugaban na kasar Sin zai gana kuma da sabuwar shugaban gwamnatin tarayyar, Angela Merkel.

Ga gwamnatin ta Sin dai, wadannan canje-canje a Jamus, ba su da wani angizo a kann huldodi tsakanin kasashen biyu. Kamar yadda ministan harkokin wajen Sin din, Li Zhaoxing ya bayyanar wa wani taron maneman labarai:-

„Ba na tsammanin cewa, Jamus na cikin wani mawuyacin hali. Abin da ke faruwa yanzu a kasar, batu ne da ya shafi harkokinta na cikin gida. A namu ganin dai, ko wa ke jan ragamar mulkin Jamus ma, za mu iya ci gaba da huldodinmu. Na tabbatar jami’an siyasar Jamus ma na sha’awar ganin cewa, mun ci gaba da inganta kyakyawar huldar zumunci da ke tsakaninmu. Dukkansu na ba da muhimmanci ga hulda da Sin.“

Babu shakka, Li Zaoxing na da gaskiya. A lokacin da ya ci zaben shekarar 1998, shugaba Schröder ya ci gaba ne da manufofin siyasar tsohuwar gwamnatin Jamus game da Sin, karkashin jagorancin Helmut Kohl, musamman ma dai a huskar tattalin arziki. Ta hakan ne kuma, a karkashin gwamnatin Angela Merkel, ba za a ga wani sauyi ba, a matsayin da Jamus za ta dauka a fannin manufofin siyasarta na ketare game da Sin din. Dangantaka tsakanin kasashen biyu dai ta yi zurfi ainun.

Ba abin mamaki ba ne kuwa, ganin cewa, Jamus ta tallafa wa Sin wajen shirya taron nan na kasa da kasa, kan samad da makamashi mai sabuntuwa kuma maras gurbata yanayi, wanda aka bude a birnin Beijing a makon da ya gabata. Kazalika kuma, a halin yanzu, daliban kasar Sin fiye da dubu 20 ne ke karatu a kafofin yada ilimi mai zurfi a nan Jamus. Har ila yau dai, za a iya lura da bunkasar cinikayya, wadda ta ribanya har sau uku, tsakanin kasashen biyu, tun da gwamnatin shugaba Schröder ta fara jan ragamar mulki a nan Jamus, a shekaru 7 da suka wuce.

Amma duk da wannan kyakyawar hulda a fannin cinikayya da tattalin arziki, wasu manazarta al’amuran yau da kullum a fannin siyasa na nan Jamus na nuna cewa, babu shakka, za a sami canje-canje a manufofin siyasar harkokin waje, idan sabuwar gwamnatin Angela Merkel ta kama aiki. Hakan kuwa zai iya shafan dangantaka tsakanin Jamus da Sin. Kamar yadda Farfesa Eberhard Sandschneider na Berlin ya bayyanar:-

„Tun da dadewa ne dai, shugaban gwamnatin tarayya mai jiran gado Angela Merkel, ta yi ta nanata cewa, idan ta hau karagar mulki za ta iy duk iyakacin kokarinta wajen ganin cewa ta inganta huldodi tsakanin Jamus da yankin ketaren tekun Atlantik, wato abin da ake nufi a nan, Amirka. To a nan kuwa, babu shakka sai duk wani sauyin da za a samu ya shafi Sin, musamman ma dai a huskar tattalin arziki da na soji.“

Batun dage takunkumin sayar wa Sin makamai, zai kasance daya daga cikin muhimman duk jigogin da za a tattauna a kansu. An dai sanya wa Sin takunkumin ne tun 1989, bayan fatattakar kungiyoyin bin tafarkin dimukradiyyan nan da gwamnatin kasar ta yi. kasashen Amirka da Japan, sun bayyana bacin ransu ga tattaunawar da aka fara a kungiyar Hadin Kan Turai, ta yunkurin dage takunkumin. A nan Jamus ma, a lokacin muhawarar da aka yi a majalisar dokoki ta Bundestag a cikin watan Ifirilun da ya gabata, shugaba Schröder ya goyi bayan dage takunkumin, yayin da Angela Merkel kuwa ta dage kan a ci gaba da shi.

To halin da ake ciki dai ke nan yanzu a matsayin Jamus game da wannan takunkumin. Sai dai, bisa dukkan alamu, a cikin shawarwarin da zai yi da mahukuntan Jamus a birnin Berlin, shugaba Hu Jintao zai takalo wannan batun. Kafin hakan ma, ministan harkokin wajensa Li Zaoxing, ya fara bayyana matsayin kasar Sin din ne da cewa:-

„Wannan takunkumin sayad da makaman da kungiyar EU ta sanya mana dai, wato muna ganinsa kamar wariya ake nuna mana a fannin siyasa. Shugabannin kasashen Turan da yawa da na tattauna da su, sun tabbatar mini cewa, hakan na da nasaba ne da al’adar da ta saura, wadda ake bi tun lokacin yakin cacar baka. Kamata ya yi a zub da duk takardun wannan takunkumin a kwandon shara.“