Ziyarar Shugaba Buhari karon farko a jihar Kano | BATUTUWA | DW | 06.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Ziyarar Shugaba Buhari karon farko a jihar Kano

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya na ci gaba da ziyarar aiki a jihar Kano, bayan tsawon lokaci da al'ummar jihar suka shafe suna kishirwar zuwansa jihar dake zaman babbar jihar da ta fi bashi goyon baya.

A wannan Larabar dai shugaban ya bude wasu manyan asibitoci da gwamnatin jihar ta Kano ta samar baya ga hanyoyi da wasu cibiyoyi da ake sa ran zai sanya musu albarka kafin kammala ziyarar tasa da ake zaton ta wuni 2 ce. Sai dai kuma da dama daga cikin al'ummar jihar na ganin cewar matsin tattalin arziki da ya addabi alummar Najeriya na daga cikin abubuwan da suka dakile armashin ziyarar.

Ziyarar shugaba Muhammadu Buhari wacce ita ce irn ta ta farko zuwa jihar tun bayan shigarsa fadar Aso Rock a matsayin shugaban kasa, ta bude sabon babi a fagen siyasar Kano dama kasa baki daya. Galibin mutane dai na ra'ayin cewar ba a yi cikar kwari ko cincirindon jama'a da aka saba yayin tarbar shugaban ba, wanda wasu ke alakanta hakan da yanayin kuncin rayuwa da ake ganin ya ta'azzara a zamanin mulkin shugaban.

Batun jamian tsaro da aka baje shi ma wani abu ne da mutane ke ganin cewar mahukunta sun aminta da cewar mutane a kufule suke kuma sukan iya yin wani yunkuri da ka iya jawowa a ji kunya. Ahmad Abdu da akewa lakabi da shekaran gwammaja ya bayyana cewar mutane sun tafi harkokinsu ba tare da damuwa da ziyarar kamar yadda aka zata ba.

Sai dai kuma masu fashin baki irinsu Abdullahi ismail kwalwa suna da imanin cewar rashin fitowar mutane kamar yadda aka zata ya faru ne kasancewar ziyarar aiki shugaban ya kawo ba ta siyasa ba.

 

Shugaba Muhamad Buhari, ya bude manyan ayyuka da suka hada da katafaren asibitin da aka yi wa wasali da kayan aiki na zamani aka kuma rada masa suna Muhammadu Buhari Specialists' Hospital dake unguwar Guginyu, da asibitin yara dake unguwar gidan Zoo, sai kuma wasu tituna da cibiyoyi daban-daban. Yayin da yake jawabi a wajen bude asibitin da aka rada wa sunansa, shugaba Buhari yayi jawabin nuna gamsuwa.

Nigeria Abuja Präsident Muhammadu Buhari (picture-alliance/dpa/W. Krumm)

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

''A yau ina farin cikin yadda gwamnatinmu ke kawo sauyi ga al'umma. Wannan asibiti wanda shi ne irinsa na farko a wannan shiyya, cikakkiyar shaida ce dake nuna yadda gwamnatin jama'a take kuma dole na yaba wa gwamnatin gwamna Abdullahi Ganduje bisa yadda ya mayar da fifita ayyukan kyautata wa alumma; ina kira ga sauran gwamnoni da su yi koyi da shi. Don haka ina rokon Allah ya albarkaci al'ummar jihar Kano, ya kuma kare su''

Shi ma a jawabinsa, gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, cewa ya yi an gina asibitin ne domin rage tururuwar neman lafiya daga Kano zuwa kasashen waje. Har ila yau kuma tawagar shugaban kasar ta kai ziyarar bangirma fadar mai martaba sarkin Kano Muhammad Sunusi na 2, har ma a jawabinsa Sarki ya yi fatan nan da wani lokaci shugaban zai dawo ya kaddamar da ayyukan gwanatin tarayya a Kano.

 

Sauti da bidiyo akan labarin