Ziyarar Schröder Ga Kasashen Asiya | Siyasa | DW | 12.10.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Schröder Ga Kasashen Asiya

Bisa ga dukkan alamu kwalliya ta mayar da kudin sabulu dangane da manufar da shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya sa gaba a ziyararsa ta yini shida ga kasashen Asiya

Schröder lokacin taron manema labarai tare da Karzai

Schröder lokacin taron manema labarai tare da Karzai

Ko shakka babu shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya gamsu da nasarar da ya cimma a ziyararsa ta yini shida ga kasashen Asiya ta la’akari da muhimmancin da wannan yanki ke da shi ga tattalin arzikin Jamus. Domin kuwa a wadannan kasashe, rawar da gwamnati ke takawa tana da muhimmanci, musamman a batutuwan ciniki da tattalin arziki kuma a saboda haka irin wannan ziyara take da muhimmanci domin bude kofar dangantakar tattalin arziki. Schröder dai ba ya sako-sako wajen tallata Jamus domin janyo hankalin ‚yan kasuwa na ketare wajen zuba jari a kasar. Bugu da kari kuma bisa ga ra’ayinsa ayyukan sarrafawa na kamfanonin Jamus a ketare abu ne dake taimakawa wajen kare makomar guraben ayyukan yi a cikin gida. A wannan ziyarar ta yini shida shugaban gwamnatin yayi kacibis da wata sabuwar manufa, inda ya gano muhimmancin da kasar Indiya ke da shi ga tattalin arzikin Jamus. Domin kuwa kawo yanzu hankali ya fi karkata ne kacokam zuwa ga kasar China, kasar da ya kai mata ziyara har sau biyar a cikin mulkinsa na shekaru shida da suka wuce tare da rakiyar gaggan ‚yan kasuwa. A halin yanzu haka an shirya wata sabuwar ziyarar da Schröder zai kai kasar China a cikin watan desamba mai zuwa. Ita kuwa Indiya, wannan shi ne karo na biyu da ya kai mata ziyara. Amma akalla shugaban gwamnatin ya farga cewar dukufa kacokam kan kasar China babban kuskure ne. Domin kuwa Indiya mai yawan mutane miliyan dubu daya da rara, wacce kuma tafi kowace kasa mai bin tafarkin demokradiyya, girma a duniyar nan tamu, ko ba dade-ko-ba-jima zata zama ja gaba a nahiyar Asiya.

Dangane da kasar Pakistan kuwa, a matsayinta na kasa mai makobtaka da Afghanistan tana da muhimmanci a matakan yaki da ta’addanci tsakanin kasa da kasa duk kuwa da cewar shi kansa shugaba Musharraf dan kama karya ne da ya dare kan karagar mulkin kasar da karfin bindiga. Wato dai dangantakar ta fi ba da la'akari ne ga siyasa a maimakon tattalin arziki kuma Musharraf bai fito fili ya bayyana goyan bayansa ga shawarar garambawul ga kwamitin sulhu na MDD ba ganin cewar ita ma Indiya tana fafutukar neman wata kujera ta dindindin a kwamitin na sulhu. Maganar ta neman dawwamammen wakilci a kwamitin sulhu na MDD dai tana taka muhimmiyar rawa a balaguron da Schröder ke yi ga kasashen ketare. Bisa ga ra’ayinsa, wannan shi ne daidai lokacin da ya kamata a aiwatar da wannan gyara domin karbar karin kasashe a tsakanin wadanda ke da ikon hawa kujerar naki, in kuwa ba haka ba za a ci gaba ne da zaman tsammanin warrabukka. A wannan balaguron dai, wanda ya hada da ya da zango a zauren taron kolin kasashen Asiya da na Turai ASEM a takaice, shugaban gwamnatin na Jamus ya samu kafar ganawa da wakilan kasashe kimanin 40, wato kwatankwacin kashi daya bisa biyar na kasashen MDD, wadanda zasu tsayar da shawara a game da manufar ta garambawul. Kawo yanzun dai kasashen Italiya da Pakistan ne ke adawa da wannan manufa, amma a baya ga haka ga alamu kwalliya ta mayar da kudin sabulu ga bukatun Jamus sakamakon kin yin na’am da tayi da yakar kasar Iraki.