Ziyarar Paparoma Francais a Afirka | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 27.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ziyarar Paparoma Francais a Afirka

Jaridun na Jamus a wannan makon sun mayar da hankali ne kan ziyarar Paparoma a Afirka da yunkurin Jamus na tura sojoji 650 zuwa kasar Mali, sai 'yan gudun hijira.

A sharhinta mai taken "Jamus na muradin dadada wa Faransa bayan harin da ya ritsa da birnin Paris" jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce shugabar gwamnatin Jamus ta yi bayani a siyasance dangane da muradin kasar na marawa Faransa baya a kokarin da take yi na yaki da tarzoma a duniya bayki daya. Sai ta ce, idan bukata ta taso za su bada tasu gudunmowa. Bisa dukkan alamu dai Berlin tana takatsantsan dangane da kiran neman goyon baya da Faransa ta nema daga sauran takwarorinta na Turai.

Hakan ba zai kasa nasaba da sanarwa da ministar tsaro Ursula von der leyen ta yi a wannan Larabar ba, na cewar Jamus za ta aike da karin sojoji 650 zuwa kasar Mali. Sai dai wannan sanarwar bata zo wa Faransa da mamaki ba, kasancewar tuni ministocin tsaron kasashen biyu suka tattauna, kuma von der leyen ta yi wa takwaranta na Faransa Jean Le Drian manufar Jamus na fadada hannunta na agaji a Mali.

Ya zuwa yanzu dai Jamus nada sojojinta 200 a karkashin shirin hadakar nan ta Tarayyar, wadanda ke ayyukan horar da takwarorinsu na Malin a yankin kudancin kasar. Daura da haka akwai sojin Jamus din10 a ayarin kiyaye zaman lafiya na MDD. Sai dai za'a mika wannan batu gaban majalisar dokokin kasar domin zartarwa.

A dangane da ziyarar da shugaban darikar roman katolika ke yi a Afirka kuwa a labarinta mai taken" Ziyara zuwa wuri mai tsini" jaridar ta Süddeutsche Zeitung cewa ta yi, rangadin aiki da Paparoma Francais ke yi a kasashen Kenya da Yuganda da Janhuriyar Afirka ta Tsakiya, kasashen dake fara da rigingimu na siyasa da kalilanci daura talauci, babban hadari ne ba wai gareshi shi kadai ba.

Gabannin barinsa fadar vatikan zuwa wannan rangadin aiki na farko da hawansa wannan mukamin dai, shugaban darikar roman katolikan bisa ga al'ada ya yi addu'ar fatan dawowa lafiya. Tuni dai Paparoma Francais ya yi ziyara mai hadari makamancin wannan zuwea kasar Israela da Palastinu da kuma Bosnia, wanda ya yi nu da cewar ya zamanto wajibi churchi ya ziyarci irin wadannan yankuna da ke kan tsini.

Ko shakka babu yana wannan ziyara ta yini shida ne a ya kasashen da talauci da cin hanci da rashwa ya musu katutuwa, daura da matsalar nan ta rikicin addini tsakanin musulmi da kristoci. Ana fatan dai hudubar zaman lafiya da bukatar darajawa juna a zamantakewa da shugaban darikar Roman Katolikan zai yi, na iya taimakawa wajen samar da zaman lafiya.

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung tsokaci ta yi dangane da mahawarar karbar 'yan gudun hijira da kuma yaki da ayyukan tarzoma a majalisar dokoki ta Bundestag. A taken sharhinta "Turai ita ce madogara" jaridar ta ceal'ummar Jamusawa na cigaba da nuna rashin gamsuwarsu da dubban 'yan gudun hijira da ke cigaba da kwararowa cikin kasar, labarin ba daban yake tsakanin 'yan siyasa ba. Yanzu haka dai akwai shakku a zukatan har su kansu manyan jam'iyyun da ke mulki.

Sai dai duk da haka shuagabr gwamnatin Jamus Angela Merkel ta samu kyakkyawan martani a jawabinta na gabatar da kasafi a majalisa, musamman a bangaren 'yan jam'iyyar kare muhalli watau The greens