Ziyarar Paparoma a kasar Myanmar | Labarai | DW | 27.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Paparoma a kasar Myanmar

Shugaban darikar Katholika na duniya Paparoma Francis a wannan Litinin ya isa kasar Myanmar a wata ziyarar da ake kallon zai karfafa guiwar kananan kungiyoyin mabiya darikar Katholika.

Da saukarsa kuwa, Paparoma ya tsunduma cikin batun rikicin na 'yan Rohingya inda kai tsaye ya gana da shugaban rundunar sojojin Myanmar Janar Min Aung Hlaing da kasashen duniya ke zarginsa da hannu a daya daga cikin rikice-rikice mafi muni da suka shafi dan Adam. Janar Hlaing shi ne shugaban aikin tabbatar da tsaro a jihar Rakhine, inda matakan da sojoji suka dauka na murkushe Musulmi marasa rinjaye ya yi sanadin tashin akalla 'yan Rohingya dubu dari shida da asirin zuwa kasar Bangaladash.

Gamayar kasashen kasa da kasa sun kwatanta rikicin yankin na Rakhine a matsayin wani yunkuri na kawar da wata al'umma daga doron kasa.Mabiya addinin Kirista da dama na fatar ziyarar ta Paparoma, za ta dubi matsalolin da masu karamin karfi ke fama da su a Myanmar.