1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Obama a ƙasashen Burma da Thailand

November 19, 2012

Shugaban Amurka Barack Obama na gudanar da ziyara a ƙasar Burma ko Myanmar domin zantawa da mahukuntan ƙasar kan batutuwa da su ka danganci demokraɗiyya.

https://p.dw.com/p/16lVN
Hoto: Reuters

Ziyarar ta shugaba Obama dai ita ce ta irinta ta farko da wani shugaban Amurka da ke an gadon mulki ya kai ƙasar ta Burma ko Myanmar, inda ziyarar ta fi maida hankali kan batutuwan da su ka dangancin yunƙurin mahukuntan ƙasar na girka tsarin demokraɗiyya da kuma zaburar da su wajen gudanar da gyare-gyare na siyasa.

A jawabin da shugaba Obaman ya yi a jami'ar Yangon, shugaban ya ce sauyi musamman a tsarin demokraɗiyya abu ne da kan taimaka wajen ciyar da ƙasa gaba kana Amurka za ta kasance mai ɗasawa da duk wata da za ta ke bin dokokin musamman na kare haƙƙin bani adama sau da ƙafa.

USA Burma Myanmar Präsident Barack Obama in Rangun bei Thein Sein
Shugaba Obama da takwaransa na BurmaHoto: dapd

"Mun gani a wurare daban-daban na duniya yadda sauyi ke bunƙasa inda aka jama'a su ka bada gudumawa. musamman ma dai in su ka san cewar ana mutunta abubuwan da su ke da muradi. Abin da zan shaidawa al'ummar Burma cewa za mu yi bakin ƙoƙarinmu wajen duniya ta saurare buƙatunsu".

A nasa jawabin shugaban na Burma Thein Sein wanda ya jinjinawa shugaba Obama dangane da ziyarar ya ce za su yi aiki tare da gwamnatin Amurka don buƙasa tsarin demokraiyyarsu da kuma kyautata hakkin bani adama, inda a cewarsa ƙasar ta ɗauki aniyar ganin ta saki fursunonin da ake tsare da su ba bisa ƙa'ida ba, hasalima gabannin ziyarar ta Obama gwamnatin kasar ta yi afuwa ga kimanin fursuna sittin da shidda ciki har da wasu fitattun 'yan siyasa.

Ita ma dai madugar 'yan adawar ta Burma Aung San Suu Kyi a nata kalaman yayin wani jabin haɗin gwiwa da ta da shugaba Obama ga manema labari cewa ta yi za su matakin da Obama ya dauka na tabbatar da samun sauyi a tsarin demokradiyyar kasar abin a yaba ne inda ta ce za su yi aki kafaɗa da kafaɗa da Amurka don kaiwa ga ci.

Tuni da wasu al'ummar ƙasar su ma a nasu ɓangaren su ka fara nuna jin daɗinsu dangane da wannan ziyara ta shugabn na Amurka da ma dai sauye-sayen da gwamnatin ƙasar ke yi musamman ma dai batun kare haƙƙin bani adama.

"An fara samun cigaba a fannin kare haƙƙin ɗan adama abunda mu ke bukata yanzu haka shi ne cigaba na tattalin arziki kuma mu na fata Obama zai taimaka wajen yiwuwar haka".

To sai dai yayin da shugabannin ƙasar ta Burma da kuma bakonsu wato shugaba Obama gami da al'ummar kasar ke tofa albarkacin bakinsu dangane da ziyarar da ma dai dangantaka tsakanin kasashen biyu, a hannu guda ƙungiyoyin kare haƙƙin bani adama da na fararen hula su ka fara sukar ziyarar ta shugaba Obama saboda a cewarsu hakan nuna cikakken amincewa ne da gwamnatin ta Myanmar duk kuwa da cewar ba su kammala gudanar da gyara ga tsarin demokraɗiyyar ƙasar ba, to sai dai Obaman ya ce ba wai amincewarsa da gwamnatin ya ke son nunawa ba, ya na son nuna cewar an samu sauye-sauyen demokraɗiyya a ƙasar ne.

Myanmar Politik Aung San Suu Kyi
Shugabar 'yan adawar BurmaHoto: dapd

Kafin isar shugaba Obama ƙasar ta Burma, ya yada zango a Thailand inda ya zanta da mahukuntan ƙasar kan batutuwa da dama inda ya jinjinawa gwamnatin firaminista Yingluck Shinawtra dangane da jajircewarta wajen baiwa tsarin demokraɗiyyar damar miƙe ƙafa da kuma aiwatar da aiyyukan cigaban al'umma.

A Talatar nan ce idan Allah ya kaimu shugaban na Amurka zai hallarci taro da za a yi ƙasar a Kambodiya na ƙungiyar ƙasashen nahiyar Asiya.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mohammad Nasiru Awal