Ziyarar Niebel a Afirka | Siyasa | DW | 14.01.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Niebel a Afirka

Sabon ministan taimakon ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirk Niebel ya kammala ziyararsa ga ƙasashen Afirka. Ute Schaeffer na cikin tawagar da tayi musu rakiya ga kuma sharhin da ta rubuta

default

Ministan taimakon raya ƙasa na Jamus Dirk Niebel a Afirka

Ko da yake da farkon fari, ba ma'aikatar taimakon raya ƙasashe masu tasowa ne Dirk Niebel yayi fatan samu lokacin da aka naɗa shi kan wannan muƙami ba, amma a halin yanzu ya bayyana gamsuwarsa da wannan matsayi bayan ziyarar farko da ya kai nahiyar Afirka. To ko shin za a samu canjin alƙibla a manufofin raya ƙasa na Jamus a ƙarƙashin jagorancinsa. Ute Schaefer dai na tattare da ra'ayin cewar ba za a samu wani canji na a zo a gani ba.

Sabon ministan taimakon raya ƙasashe masu tasowan na Jamus dai ya lashi takobin bai wa manufofin raya ƙasar wani sabon fasali mai sassauci da ya haɗa da ƙarfafa dangantakar manufofin raya ƙasar da na ƙetare da kuma na cinikin ƙasa da ƙasa. A ganinsa taimako don dogara da kai shi ne mafi a'ala. To sai dai kuma ba 'yan jam'iyyar Free Democrats dake da sassaucin manufofin siyasa ne suka fara ƙiƙiro wannan manufa ba, kamar yadda shi kansa Dirk Niebel ya nunar. Hatta ita kanta magabaciyarsa akan wannan muƙami ta durfafi wannan alƙibla. Ba za a samu wani canji na a zo a gani ba, saboda dalilai da dama. Domin kuwa akwai ɓangarori da yawa da game da matakan taimakon raya ƙasar dake gudana ƙarƙashin yarjeniyoyi na ƙasa da ƙasa. Waɗannan ɓangarorin sun shafi wasu manufofin da aka wajabta kan ƙasashen dake da hannu a waɗannan yarjeniyoyi, kuma Jamus ta taka muhimmiyar rawa wajen cimmusu. Ƙasar tana da muhimmanci matuƙa ainun a manufofin taimaƙon raya ƙasashe masu tasowa na ƙasa da ƙasa. A baya ga haka su kansu ƙungiyoyin taimako masu zaman kansu suna da wata ƙaƙƙarfan matsayi da tasiri, inda aka wayi gari sun zama tamkar masana'antu ne masu zaman kansu kuma kowace masana'anta na bakin ƙoƙarinta wajen rabonsa a kasuwa. Dirk Niebel na sane da dukkan waɗannan abubuwan. A sakamakon haka matakin farko da ya ɗauka shi ne garambawul a cikin gida, inda yake ƙoƙarin haɗa kan dukkan ƙungiyoyin taimako na Jamus ƙarkashin tuta guda a cikin gaggawa. Yana fatan hakan ya tabbata a cikin watanni shida masu zuwa. Kazalika nan gaba za a samu wata dangantaka ta ƙut-da-ƙut game da manufofin raya ƙasa da na ƙetare da kuma harkokin ciniki na ƙasa da ƙasa. Domin dukkan waɗannan ma'akatu guda uku suna ƙarƙashin jam'iyyar Free Democrats ne. A dai ziyararsa ga Afirka Dirk Niebel ya saurari abokan shawararsa da sosai ba tare da ɗaukar wani tsayayyen ra'ayi tun da farko ba. Ya kuma ce ba ya sha'awar wata manufa ta shiga shara ba shanu a matakan taimakon raya ƙasa. Ba shakka hakan zai share hanyar samun kyakkyawar ma'amalla tsakanin masu bayarwa da masu karɓar taimakon.

Mai fassara: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu