Ziyarar Hillary Clinton a Afirka | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 09.08.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ziyarar Hillary Clinton a Afirka

Jaridun sun fi mayar da hankalinsu akan rangadin wkanaki 11 da skatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ke kaiwa Afirka

default

Hillary Rodham Clinton a Kenya

A wannan makon mai ƙarewa ma dai jaridun na Jamus sun rubuta rahotanni da dama akan nahiyarmu ta Afirka, to amma akasarinsu sun fi mayar da hankali ne akan ziyarar aiki da sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ke kaiwa Afirka.

A wani rahoto da ta fara da cewa sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta ƙaddamar da rangadi a Afirka a daidai wurin da shugaba Barak Obama ya kammala a Ghana a watan da ya gabata, jaridar Tageszeitung ta ce:

Tare da kira da a samar da kyakkyawan shugabanci Clinton ta buɗe taron hulɗar cinikaiya tsakanin Afirka da Amirka karo na takwas a birnin Nairobin ɗin Kenya. Tana mai cewa samun bunƙasar tattalin arziki mai ma´ana a Afirka ya dogara akan shugabanni na gari waɗanda ke yaƙi da cin hanci da rashawa amma masu radin mulki na adalci da bin doka don samarwa jama´a kyakkyawan sakamako. Jaridar ta ce wannan furucin shaguɓe ne ga gwamnatin Kenya wadda ta karɓi baƙoncin taron, wadda a watan jiya ƙungiyar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Transparency International ta ce ta fi fama da matsalar cin hanci a tsakanin ƙasashen Afirka Ta Gabas.

Kenia USA Außenministerin Hillary Clinton in Nairobi

Nahiya a cikin rikici, wannan shi ne taken rahoton da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta game da rangadin kwanaki 11 da Clinton ke kaiwa ƙasashen Afirka da suka haɗa da Kenya, Afirka Ta Kudu da Najeriya mafiya ƙarfin tattalin arziki a Afirka. Ta ce ban da kalamai masu daɗin ji da ta furuta game da sabuwar manufofin Amirka akan Afirka, amma ganin yadda gwamnatinta ta duƙufa wajen tinkarar matsalolin tattalin arziki da rikice-rikice a Afghanistan da kuma yankin Gabas Ta Tsakiya, zai yi wuya Amirka ta ba wa nahiyar ta Afirka wata kulawa da ta dace.

Frauen demonstrieren in Khartum, Sudan

Lubna Hussein, a dama, lokacin zanga-zanga a Khartoum, Sudan

Lubna Ahmed Hussein ta ƙuduri aniyar yaƙi da dokar yiwa mata bulala saboda abin da aka kira sanya tufafin da ba su dace ba. Wannan shi ne layin farko da har wayau jaridar ta Franfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta akan shari´ar nan da ake wa ´yar ƙasar Sudan Lubna Hussein akan yi wata shiga da ba ta dace ba. Jaridar ta ce bisa ga dukkan alamu Lubna na kan hanyar kafa tarihi a Sudan na ganin an soke wannan doka. A cikin watan Satumba ne za a ci-gaba da shari´ar da ake wa Lubna.

Wieder deutsches Schiff von Piraten gekapert

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta mayar da hankali ne akan sakin jirgin ruwan ɗaukar kaya na Jamus a Somaliya bayan an bawa ´yan fashin kuɗin fansa. Jaridar ta rawaito ´yan siyasar ƙasar na yin kira da tarayyar Turai da ta ɗauki tsauraran matakai akan ´yan fashin jirgin ruwa a Afirka. Wasu ´yan jam´iyun CSU da SPD sun yi suka da kakkausan lafazi game da bawa ´yan fashin jirgin ruwan na Somaliya kuɗin fansa. A tsakiyar makon ne aka saki jirgin ruwan da ma´aikatansa 24 bayan sun shafe watanni huɗu a hannun ´yan fashin.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadisou Madobi