1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gabas ta Tsakiya: Ziyarar Antony Blinken

Mahmud Yaya Azare LMJ
January 30, 2023

Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya fara wata ziyarar aiki a yankin Gabas ta Tsakiya daga Masar, a daidai lokacin da rikici ya yi kamari tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

https://p.dw.com/p/4MsUK
Isra'ila | Tel Aviv | Ziyara | Antony Blinken | Amirka
Sakataren harkokin kasashen wajen Amirka Antony Blinken ya isa birnin Tel AvivHoto: Ronaldo Schemidt via REUTERS

Tuni dai sakataren harkokin wajen Amirkan Antony Blinken ya isa Masar, a wani rangadin da ya fara a yankin na Gabas ta Tsakiya da zai kaishi Isra'ila da yankunan Falasdinawa. Baya ga wadannan wurare, Blinken zai kuma kai ziyara kasar Jordan a kokarin da kasarsa ke yi na kwantar da wutar rikicin da ke ci gaba da ruruwa tsakanin Isra'ila da Falasdinu. A ziyarar da ya faro daga kasar Masar, sakataren harkokin wajen na Amirka Antony Blinken ya bi sahun jerin jami'an diplomasiyar kasarsa da ke ta kai gwauro suna kai mari a kwanakin baya-bayan nan a yankin Gabas ta Tsakiyar.

Karin Bayani: Ziyarar ministan tsaron Isra'ila a Kudus

Cikin wadanda suka kai irin wannan ziyara dai, har  da shugaban Hukumar Leken Asirin Amirka ta CIA da tawagar wasu jakadu na musamman da suka ziyarci yankin domin kwantar da wutar rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinawa da ke kara yin kamari musamman bayan wani samame da Isra'ila ta kai yankin Jenin na Falasdinawa. Wannan samame dai ya halaka wasu mutane 10 wadanda ta ce 'yan ta'adda ne da ke shirin kai mata hare hare, yayin da suma wasu matasan Falasdinawa suka bude wuta kan wani gidan bautar Yahudawa har ya kai ga halaka mutane takwas.

Isra'ila | Hari | Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin NetanyahuHoto: Ronen Zvulun/REUTERS

A yayin da yake jawabi a birnin Alkahiran Masar, Blinken din ya bayyana irin muhimmancin da Masar ke da shi wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin baki daya. A nasa bangaren ministan harkokin wajen Masar Sameh Shukry ya nemi Amirkan da ta sake matsin lamba kan gwamnatin masu tsaurin ra'ayi da Benjamin Natenyahu ke jagoranta, domin komawa kan tattaunawar zaman lafiyar da za ta kai ga kafuwar kasar Falasdinu. Baya ga batun rikicin Isra'ila da Falasdinawa Blinken ya nemi hadin kan Masar domin sake mayar da Iran saniyar ware, kasar da ya bayyana da babbar barazanar tsaro a Gabas ta Tsakiya.

Karin Bayani: Cece-kuce kan kalaman Mahmoud Abbas a Jamus

Haka kuma ya nemi kasar ta Masar da ta ci gaba da taka kyakkywar rawa wajen ganin an sasanta bangarorin da ke rikici a kasashen Libiya da Sudan, domin ganin an kai ga shirya ingantancen zabe a kasashen. Kafin ya wuce birnin Tel Aviv na Isra'ila dai, sai da sakataren harkokin wajen na Amirka ya gana da matasan Masar masu fafutukar neman sauyi. A yayin ganawar tasu, ya nuna musu muhimmancin sauraronsu a duk wani ci-gaban da ake fatan samar wa a yankin.