Ziyarar al-Sisi a tarayyar Jamus | Siyasa | DW | 03.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar al-Sisi a tarayyar Jamus

Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi na kasar Masar ya fara ziyarar aiki Jamus daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsin lamba kan take hakkin bil Adama.

Tun a cikin watan Satumbar shekarar da ta gabata ce dai jamus din ta baiwa Al-Sisi goro na gayatta don ganawa da mahukunta Jamus duk kuwa da irin sabanin ra'ayin da ake samu tsakanin gwamnatin Angela Merkel da Masar din. Jamus dai na daukar Masar a matsayin kasa mai muhimmancin gaske a yankin gabas ta tsakiya.

Makasudin gayyatar al-Sisi zuwa Jamus

PK Merkel und Sisi in Berlin

Shugaba Abdel Fatah al-Sisi tare da takwararsa ta Jamus Angela Merkel.

Tun farko gwamnatin kasar ta Jamus ta danganta ba da goron gayyatar da samun sahihin zabe a matsayin sharadin gayyatar, amma daga bisani ta yi watsi da haka. A cikin watan Maris, ministan kula da tattalin arziki Sigma Gabriel kana mataimakin shugaban gwamnati daga jam'iyyar SPD ya mika goron gayyatar.

Matakin ya zo bayan wasu kasashen Turai sun gayyaci Shugaba al-Sisi na kasar ta Masar, inda a watan Satumban da ya gabata ya ziyarci Italiya da Faransa, sannan a watan Afrilu ya kai ziyara kasar Girka.

Sukar lamirin Jamus kan gayyato al-Sisi
Sai dai a cewar Norbert Lammert da ke zama shugaban majalisar dokokin kasar Jamus ta Bundestag, gwamnatin kasar ta Masar ta wuce makadi da rawa wajen yanke hukunci kisa ga 'yan adawa inda ya ke cewar "an yanke wa mutane da dama hukuncin kisa yayin zaman shari'ar da ake tababa, kuma wadannan sun hada da jiga-jigan 'yan adawa."

Kairo Prozess gegen Anhänger der Muslimbrüder 2.2.2015

Ana zargin gwamnatin al-Sisi da tauye 'Yancin mutane musamman a bangaren shari'a kasar.

Lammert ya kara da cewa bai ga ta inda za su yi wata hulda ba idan aka duba abin da ke faruwa a kasar ta Masar. Tuni da masana harkokin siyasa a Jamus din irin su Franziska Brantner su ka fara sukar wannan ziyara ta al-Sisi a Berlin inda ta ke cewar "haka babban abu ne mai mahimmanci ga al-Sisi wanda zai gana da daya daga cikin shugabanni masu karfin fada aji a duniya. Ina tsammani bai dace a yi wannan gayyata ba."

Gwamnatin Jamus ta soki matakin ba-sani ba-sabo da gwamnatin Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi take dauka kan 'yan adawa musamman na kungiyar 'Yan Uwa Musulmai a kasar ta Masar.

Sauti da bidiyo akan labarin