Ziyara Jan Egeland a ƙasar Sudan | Labarai | DW | 03.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Jan Egeland a ƙasar Sudan

Mataimakin Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia mai kulla da harakokin bada agaji, ya fara ziyara aiki, a nahiyar Afrika.

A yanzu haka Jan Egeland, na Juba babban birnin yankin kudancin Sudan.

A hira da yayi da manema labarai, Sakataren ya nuna damuwa, a game da halin da ake ciki a yanki Darfur, inda rikici ya ƙi ci ya ƙi cencewa.

Jami´in, ya ce yanayin tashe tashen hankulla, a yankin na sa tarnaƙi, ga ayyukan bada agaji, na ƙungiyoyin Majalisar Ɗinkin Dunia.

Egeland, yayi kira da babbar murya, ga Majalisar Ɗinkin Dunia, da ta tura dakarun kwantar da tarzoma cinkin gaggawa a wannnan yanki, domin ƙarfafa rundunar ƙungiyar Tarayya Afrika.

A ɗaya wajen, ya kiri ƙungiyoyin bada agaji na ƙasa da ƙasa, da kuma ƙasashe masu hannu da shuni, da su cika alƙawuran da su ka ɗauka, a game da yankin kudancin Sudan, inda ƙura ta laffa, a sakamakon yarjejeniyar da a rattaba hannu a kai, bara tsakanin gwamnatin da yan tawaye.

Saidai duk,da wannan yarjeneniya, da kuma alkawuran bada kudade, da aka ɗauka, har yanzu, wannan yanki na fama da matsaloli masu yawa.

Kazalika, babu kwanciyar hankali, a dalili da hare haren da ƙungiyar tawayen LRA ,ta ƙasar Uganda ke kaiwa a yanki.