Ziyara Hu Jin Tao a nahiyar Afrika | Labarai | DW | 31.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Hu Jin Tao a nahiyar Afrika

Shugaban ƙasar Sin Hu Jin Tao, ya fara rangadi a nahiyar Afrika.

A mataki na farko ya sauka yammacin jiya a ƙasar Kamaru inda ya samu tarbe na karamci.

Nan gaba a yau ne,zai gana da shugaban ƙasa Paul Biya, inda a ka tsara rattaba hannu a kan yarjeniyoyi daban daban, ta fannin harakokin saye da sayarawa tsakanin ƙasashen 2.

Bayan ƙasar Kamaru, Hu Jin Tao zai ziyarci ɗaya bayan ɗaya, ƙasashen Liberia, Sudan, Zambia, Namibia, Afrika ta Kudu, Mozambique, da tibirin Seyschelles.

Tun hawan sa kan karagar mulki a shekara ta 2003, wannan shine karo na 3, da shugaba Hu Jin Tao, ke ziyartar Afrika, nahiyar da ya maida a tsaka-tsakiyar siyasar ci gaban harakokin tattalin arzikin Sin.