Ziyara Frank Walter Steinmeir a Afrika | Labarai | DW | 01.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Frank Walter Steinmeir a Afrika

Ministan harakokin wajen Jamus, Franck Walter Steinmeir, ya fara ziyara aiki a taraya Nigeria.

Bayan tarben karamci da ministan ya samu daga al´ummomin Nigeria, tawagogin ƙasashen 2, su ka shiga tantanawa.

Sun fara da bitar mu´amilar cinikaya a tsakanin Jamus da Nigeria, wadda su ka gano cewar, ta na tafiya salin-alin, to saidai tawagogin 2, sun nunar da cewa, akwai hanyoyin ƙara bunƙasa wannan hulɗoɗi, a wasu ɓangarori daban na dabra da man petur.

A shekara da ta gabata,saye da sayarwa tsakanin Jamus da Nigeria, ya samar da kuɗaɗen da yawan su ya kai kussan Euro milion dubu ɗaya da rabi.

Gobe idan Allah ya kai mu, Frank Walter Steinmeir zai gana da shugaban ƙasa Al haji Umaru Musa Yar Aduwa.

Zai kamalla wannanziyara da kasar Ghana, inda zai tantana da shugaban ƙungiyar tarayya Afrika, John Kuffor.

Shugabar gwamnatin Jamus Angeler Merkel,ta bayyana buƙatar ƙarawa Afrika taimakon raya ƙasa, domin tallafa mata, ta fita daga ƙangin talaucin da ta ke fama da shi.