1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara C.Rice a Russia

May 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuLW

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, na ci gabada ziyara aiki a ƙasar Russia.

A sahiyar yau, ta gana da wakilan ƙungiyoyin fara hulla, inda su ka tantanana batutuwan kare haƙƙoƙin bani a wannan ƙasa da ta yi ƙaurin suna, ta wannan fanni.

Condoleesa Rice, ta bayyana rashin gamsuwar gwammnatin Amurika, a game da yadda fadar mulkin Kremblin, da ke birnin Mosco,ta tattare dukkan mulki cikin hanun ta, a game da haka, ta yi kira ga hukumomin ƙasar, su ƙara girmama demokraɗiya, ta hanyar damawa da sauran sassa na al´ummar ƙasa.

Nan gaba a yau Rice za ta gana, da shugaban ƙasa Vladmir Poutine, to saidai masharanta, na nunar da cewa da alamun za su tabka mahaurori masu zafin gaske, ta la´akari da shiga sharo ba shanun, da hukumomin Russia, ke zargin Amurika na yi ,a harakokin su na cikin gida.

Babban burin wannan ziyara, shine na ɗinke ɓarakar da ta kunno kai, tsakanin ƙasashen 2, masu faɗa aji ,a game da batutuwa daban-daban, na siyasa da kuma diplomatiar dunia.