1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Condoleesa Rice a kasar Labanon

February 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bv75

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, na ci gaba da ziyara aika a yankin gabas ta tsakiya.

A yau ta kai ziyara ba zata a ƙasar Labanonon da nufin a cewarta ƙara ƙarfin gwiwa ga faɗi ka tsahin da ƙasar ke yin a samara da cikkaken yanci.

Rice ta yi ganawar farko da Cardinal Nasrallah Sfeir, shugaban christocin ƙasar Labanon.

Saidai a wannan ziyara, sakatariyar harakokin wajen ba za ta haɗuwa ba da shugaban ƙasar Emil Lahud da Amurika ke zargi da zama karan farautar Syria.

Condoleesa Rice ta yi anfani da wannan dama inda ta ƙara jaddada buƙatar Syria, ta bada haɗin kai ga komitin bincike a kan mutuwar tsofan Praminista Rafik Hariri, a shekara da ta gabata, kissan da, a ke tuhumar hukumomin Syria da hannu a ciki.

A ɗaya hannun, Condoleesa Rice, ta gana da Praminista, Fouad Siniora da kuma shugaban rukkunan yan majalisun dokoki masu rinjaye, da ke adawa da ƙasar Syria, wato Walid Jumblat, da Saad Hariri.