Zimbabwe na jiran sakamakon zabe | Siyasa | DW | 17.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zimbabwe na jiran sakamakon zabe

Jami'an hukumar zaben Zimbabwe, na ci gaba da kidayar kuri'ar raba gardama da al'umma suka kada akan daftarin sabon kundun tsarin mulkin kasar da aka jima ana jira

Duk da cewar mutane kalilan ne suka fita domin kada kuri'unsu a zaben na ranar asabar, akwai alamun cewar dafrin zai samu karbuwa, kasancewa dukkan manyan jam'iyyun siyasar Zimbabwe suna goyon bayan amincewa da shi.

Akasarin mutane dai sun kauracewa zaben, abunda acewarsu basu da kyakkyawar masani dangane da abinda daftarin ya kunsa. An dai fuskanci tangarda daban daban kafin a akai ga cimma kammala rubuta kundin, daya dauki shekaru uku.

Dr. Solomon Zwana shine ke shugabantar gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu dake marawa zabe baya, wadanda suke zama masu sa ido akan zaben raba gardamar.

Ya ce " mutane kalilan ne suka fita kamar yadda ake zato. Akwai koken cewar ba'a bawa mutane isasshen lokacin nazarin kundin ba. Wasu ma na cewar basu ga daftarin da idanunsu ba, suna dogaro ne da kiran da masu goyon bayan daftarin ke musu na cewar su kada kuri'ar amincewa".'

Karancin lokacin nazarin Kundin

Duk yunkurin da masu radin kare demokradiyya suka yi, na ganin cewar an dage zaben, domin bawa mutane isasshen lokacin nazarin daftarin mai shafuna 150 ya ci tura. Sabon kundin tsarin mulkin Zimbabwen dai, ya kasance sharadin da shugabanin kasashen yankin suka bayar, na tabbatar da sahihin zabe da zai kawo karshen gwamnatin hadakan kasar. Babban sakataren kungiyar raya ci gaban kasashen kudancin Afrika ta SADC Tomaz , Salomao, ya bayyana muhimmancin zaben na kri'ar raba gardamar ta ranar asabar.

A street vender reads an ad in a local news paper in Harare on March 14, 2013 calling on Zimbabweans to vote yes for the constitutional referendum to be held in country over the weekend. Zimbabwe's Prime Minister Morgan Tsvangirai on March 12 challenged the claims of President Robert Mugabe's supporters that international observers would not be allowed to monitor upcoming elections. Beleaguered Zimbabweans will on Saturday vote on a new constitution that would, for the first time, put a definite end date on Robert Mugabe's controversial rule. AFP PHOTO / ALEXANDER JOE (Photo credit should read ALEXANDER JOE/AFP/Getty Images)

kidayar sakamako

" Wannan kuri'ar raba gardama na bangaren yarjejeniyar siyasa ta duniya, kuma yana da muhimmanci a mataki na gaba, wanda shine mafi muhimmanci.Zai kasance cikin tarihin Zimbabwe, muna fatan jama'a zasu taka rawar da zata samar musu da kyakkyawar makoma".

Zaben dai ya fuskanci kalubale daga kotuna, kasancewar kungiyoyi masu zaman kansu sun yi kokarin dage shi, domin samun karin lokacin nazarin daftarin. Shugaba Robert Mugabe yana da amsa mai sauki ga wannan. Bayan kada kuri'arsa, ya bayyana cewar, 'yan kasar ne suka rubuta daftarin kundin, domin haka basa bukatar wani lokaci na musamman na sake yin nazarinsa. A dangane da hana masu sa ido na yammacin turai shiga kasar ganin zaben raba gardamar dama zabe mai zuwa kuwa, Mugabe yana da ta cewa.

" Turawa da Amurkawa sun kakaba mana takunkumi, adangane da haka ne mu ma zamu yi harkarmu ba tare da su ba, kamar yadda suka yi watsi da mu

Ra'ayoyi sun banbanta kan zaben

Yawancin masu zaben dai sunyishi ne bisa shakku. Ga ra'ayon wasu da suka kada kuri'unsu a birnin Harare.

Zimbabwe Prime Minister and MDC leader Morgan Tsvangirai speaks to church leaders who were gathered at his offices during a meeting focused on the final draft constitution in Harare on March 15, 2013. Zimbabweans set to vote on a constitutional referendum on March 16 and crunch elections expected in June or July. AFP PHOTO / JEKESAI NJIKIZANA (Photo credit should read JEKESAI NJIKIZANA/AFP/Getty Images)

Morgan Tsvangirai

" Ina muradin taka rawa a shirin gyaran kundin tsarin mulki na ainihi, wanda zai sauya tsarin kundinmu domin kare hakkin jama'a, kamar na kasashen Venezuela ko Afrika da kudu".

"Na jefa kuri'ar amince saboda mun so tsara kundinmu da kanmu, tun samun 'yancin mulkin kai muna amfani ne da kundin mulkin Lancaster house".

Yarjejeniyar Lancaster house ta shekara ta 1979, kundi ne na samun 'yancin mulkin kai daga Britaniya.

Da zarar an kammala kidayan kuri'un tare da amincewa da sabon kundin tsarin mulkin, ana saran Zimbawe zata gudanar da zaben kasa baki daya tsakanin watannin yuli zuwa october, wanda shine zai kawo karshen gwamnatin hadaka ta jeka na yika ta shugaba Mugabe da priminista Morgan Tsvangirei da aka kafa tun a shekara ta 2009.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Pinado Abdu Wala

Sauti da bidiyo akan labarin