Zimbabuwe: Karuwar kamen ′yan adawa | Labarai | DW | 04.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zimbabuwe: Karuwar kamen 'yan adawa

Shugaban Zimbabuwe ya ayyana babbar jam'iyyar adawar kasar a matsayin ta ta'addanci, tare da lasar takobin cigaba da kamen 'yan adawa da masu sukar manufofin gwamnati.

A jawabinsa ta gidan talabijin na kasar a wannan Talatar, shugaba Emmerson Mnangagwa ya bayyana masu sukarsa a matsayin fitinannu da basa son zaman lafiya, wadanda ya zamanto wajibi a dauki mataki a kansu.

Tun a makon da ya gabata ne dai aka fara kamen, bayan da jami'an soji da na 'yan sandan Zimbabuwen suka tarwatsa gangamin adawa da Mnangagwa. Gwamnatin dai na zargin hadin baki da makiyan kasar daga ketare.

Jawabin na Mnangagwa na zuwa ne adaidai lokacin da gwamnatinsa ke fuskantar suka na cikin gida da ketare dangane da karuwar batutuwan take hakkin bil adama.