Zimbabuwe: Digirin Grace Mugabe na boge ne | Labarai | DW | 08.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zimbabuwe: Digirin Grace Mugabe na boge ne

Wani bincike da aka gudanar a kan uwargidan tsohon shugaban kasar Zimbabuwe Grace Mugabe na cewa ta mallaki wasu filaye da kuma shedar karatun kammala karatun digiri ta hanyar da ba ta dace ba.

A sanarwar da hukumomin kasar suka fitar a wannan Litinin, hukumar da ke yaki da rashawa ta yi bayanin yadda binciken ya gano cewa Missis Mugabe ba ta bi ka'idojin jami'ar ba wajen samun shedar karatun Digiri da ta samu ba, hakazalika  ta yi amfani da karfin iko wajen mallakar filayen da ta gina wani katafaren wurin shakatawa a yankin Mazowe. Hukumar ta ce ta mika sakamakon binciken gaba tunda ba ta da hurumin kama Grace Mugabe bisa wadannan laifuka.

A bara ne aka hambarar da gwamnatin Robert Mugabe na fiye da shekaru talatin a wani juyin mulki da sojoji suka yi bayan rikicin da ya biyo bayan korar mataimakinsa Emmerson Mnangagwa a kokarin share wa uwargidansa Grace fage don tsayawa takara da zummar maye gurbin maigidanta.