1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe: An yi jana'izar Mugabe

Ahmed Salisu
September 28, 2019

A wannan Asabar din (28.09.2019) aka gudanar da jana'izar tsohon shugaban Zimbabuwe Robert Mugabe wanda ya rasu a farkon wannan watan na Satumba a wani asibiti a kasar Singapore.

https://p.dw.com/p/3QQL4
Simbabwe Beisetzung Robert Mugabe
Hoto: Reuters/P. Bulawayo

An dai binne Mugabe din ne a kauyensu da ake kira Kutama da ke da tazarar kilomita 90 yamma da babban birnin kasar Harare, sai dai masu aiko da rahotanni sun ba a yi wani gagarumin biki a lokacin da aka binne shi din.

Mazauna kauyen dai sun yi ta rera wakoki na jinjina da kuma bankwana da tsohon shugaban wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 30 kafin daga bisani a yi wani juyin mulki a shekerar 2017 wanda ya raba shi da kujerarsa.

Gabannin jana'izar tasa dai, an yi ta kai ruwa rana kan idan za a binne shi inda hukumomi suka ce suna so a binne shi a wata makabarta da ake binne gwarzayen kasar a birnin Harare, yayin da iyalansa suke ce suna so su mutunta zabin da yi na son a yi masa sutura shi kusa da kabarin gyatumarsa a kauyensu na Kutama, zabin da gwamnatin kasar daga baya ta amince da shi.