Zida ya tattauna da babban sarkin Burkina | Labarai | DW | 04.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zida ya tattauna da babban sarkin Burkina

Isaac Zida na ci gaba da lalubo hanyoyin mayar da mulkin Burkina Faso ga farar hula cikin ruwan sanyi kamar yadda Kungiyar Gamayyar Afirka ta bukata.

Shugaban mulkin sojan Burkina Faso Laftana-Kanal Isaac Zida ya yi ma sarkin gargajiya mafi daraja na kasar alkawarin mika wa farar hula mulki domin gudanar da rikon kwarya bayan saukar Blaise Compaore ba girma ba arziki. Shi dai shugaban ya yi tattaki ne zuwa fadar sarki Mogho Naba saboda karfin fada a jin da ya ke da shi tsakanin kabilar da ta ke da rijaye a Burkina Faso.

Sannan kuma ya tattauna da shugaban kotun tsarin mulki wanda ake ganin cewar shi ne zai shugabancin kasar kamar yadda kundin tsarin mulkin ya tanada sakamakon tserewa da kakakin majalisar dokoki ya yi.

Wadannan tattaunawar na zuwa ne kwana daya kafin ziyarar da shugabannin kasashen Senegal Macky Sall da na Najeriya Goodluck Jonathan da kuma na Ghana John Mahama za su kai birnin Ouagadougou na Burkina Faso domin nazarin hanyoyin da za a mayar da mulki hannun farar hula.

Kungyiar Gamayyar Afirka ta dibar wa sojoji wa'adin makwani biyu don mika mulki ga farar hula idan suna so su kaucewa fishin hukumar.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu