1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Mali: Kowa na ikirarin nasara

Abdul-raheem Hassan
August 13, 2018

Magoya bayan 'yan takarar shugaban kasa Ibrahim Boubakar Keita da Soumaila Cisse, na murnar lashe zaben gabannin bayyana sakamakon a hakumance.

https://p.dw.com/p/334hI
Mali Amtsinhaber Keita Favorit bei Präsidentenstichwahl
Hoto: Reuters/L. Gnago

Bayan kammala zagaye na biyu na zaben, dukkannin bangarorin biyu na zargin juna da magudi da ma tashin hankali a wasu yankunan kasar. magoya bayan kwane daga cikin 'yan takarar biyu sun fara murnar lashe zaben a bisa dogaro da alkaluman bayan fage, kamar yadda wata a hedikwatar dan takara Ibrahim Boubacar Keita ke bayyana muranarta, inda ta ce: " Muna cike da farin ciki game da sakamakon da muka samu, dan haka muka soma shagulgulan samun nasara. Muna mika godiyarmu ga 'yan kasar Mali da suka zabi IBK, domin wannan dan takaramu babbar sa'a ce ga makomar matasa a Mali"

Mali Amtsinhaber Keita Favorit bei Präsidentenstichwahl
Hoto: Reuters/L. Gnago

Suma magoya bayan madugun 'yan adawa Soumaila Cisse sun dau lokaci suna murna a hedikwatar jam'iyyar dan takarar su, inda suna kade-kade da raye-rayen murnar lashe zaben da suke ikirari.Nouhoun Togo shi ne sakataren sadarwar dan takara Soumaila Cisse: "Muna cikin farin ciki kamar yadda kuke gani, domin sakamakon farko da ke zo mana daga ciki da ma wajen kasar Mali, na nuni da cewa dan takararmu ya yi wa shugaba IBK fintinkau. Da ma mun yi imani da hakan za ta faru , domin mun yi gwagwarmaya domin ceto kasar Mali daga wannan kangi."

Mali Stichwahl Soumaïla Cissé
Hoto: DW/K. Gänsler

Hukumar zaben kasar Mali ta soma tattara kuri'u da kidayarsu, sai dai haryanzu hukumar ba ta bayyana wani sakamako a hukumance ba. Amma ta yi alkawarin fitar da sakamakon zaben cikin lokaci. Duk dai wanda ya lashe zaben tsakanin 'yan takarar biyu da suka je zagaye na biyu, za su fuskanci matsalolin tsaro da matsalar tattalin arziki da kasar ke ciki.