Zartar da hukuncin kisa a Indonesiya | Labarai | DW | 28.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zartar da hukuncin kisa a Indonesiya

Hukumomin kasar Indonesiya sun zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutane takwas da suka samu da fataucin hodar iblis a kasar.

An zartar da hukuncin kisan ne dai ta hanyar bindige mutanen takwas daga ciki har da 'yan Najeriya hudu da 'yan Brazil biyu da 'yan Ostreliya biyu. An bindige mutanen ne da misalin karfe biyar agogon GMT wato karfe 12 na dare kenan a kasar ta Indonesiya. Saidai an dage matakin zartar da hukuncin a wata mata 'yar kasar Philippine mai suna Marie Jean wacce itama ke cikin mutanen da aka kama da wannan laifi.