1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ana zargin tsohon shugaban Jamhuriyar Nijar da karya ka'ida

Gazali Abdou Tasawa SB
May 14, 2021

A Jamhuriyar Nijar wani cece-kuce ya taso tsakanin 'yan adawa da magoya bayan tsohon Shugaba Mahamadou Issoufou kan wani filin gwamnati da 'yan adawa ke zargin tsohon shugaban ya saye a birnin Tahoua ba bisa ka'ida ba.

https://p.dw.com/p/3tOXO
Demokratische Republik Kongo Kinshasa | Nigerianischer Präsidenten Mahamadou Issoufou
Hoto: Presidence RDC/G. Kusema

Tuni ma dai 'yan adawa suka shigar da koke a gaban kotun kula da kashin kudin gwamnati wacce ta bayyana kadarorin tsohon Shugaba Mahamadou Issoufou lakcin saukarsa daga mulki domin ta bayar da karin haske kan yadda shugaban ya mallaki wannan fili.

Wannan cece-kuce dai ya taso bayan da kotun da ke kula da yadda aka aiwatar da harkokin kudi a ma'aikatun gwamnati wato Cour des Comptes ta wallafa kamar yadda doka ta tanada dukiya da kuma kadarorin tsohon shugaban kasar Nijar a karshen wa'adin mulkinsa. Daga cikin kadarorin da tsohon shugaban ya mallaka, kotun ta zano wani fili da ya mallaka a birnin Tahoua wanda amma kotun ba ki ta yi cikakken bayani kan takardunsa ba, wanda ya sanya adawa ke zargin da gangan ne aka yi shi da nufin boye wa 'yan kasa taka dokar da tsohon shugaban ya yi na sayen filin ba a kan ka'ida ba.

Karin Bayani:Mahamadou Issoufou na shirin mika mulki

Niger | Präsidentschaftswahlen in Niamey | Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

To sai dai da take mayar da martani kan wannan zargi na ‘yan adawa kan tsohon shugaban kasa, jam'iyyarsa ta PNDS Tarayya ta bakin kakakinta Malam Assoumana Mahamadou ta ce zargin da 'yan adawar suke ba shi a tushe kuma bita da kullun siyasa ne kawai da nufin shafa wa tsohon shugaban kasar kashin kaji.

Kawo yanzu dai kotun ta cour des compte wacce ta bayyana dukiya da kadarorin tsohon shugaba Mahamadou Issoufou a lokacin saukarsa daga mulki kamar yadda doka ta tanada ba ta ce komi ba a game da bukatar 'yan adawar, inda kuma yanzu 'yan kasa suka zura mata ido suka amsar da za ta bayar a kan wannan batu.