Zargin tilasta yin karya kan kisa a Ruwanda | Labarai | DW | 02.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zargin tilasta yin karya kan kisa a Ruwanda

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta zargi jami'an gwamnati da na tsaro a Ruwanda da laifin daure wasu iyalai saboda kin bada labaran karya kan dalilan mutuwar 'yan uwansu.

A cewar kungiyar jami'ai a Ruwanda na yin barazana ga iyalai don tilastasu su ce ba jami'an tsaron gwamnati ba ne suka kashe musu 'yan uwansu.

Hukumar kare hakkin jama'a a kasar ta Rwanda ta kalubalanci rahoton na Human Rights Watch inda ta ce wasu da ake cewa sun mutu a rahoton da kungiyar ta fitar suna nan a raye, kuma ma da yawa rashin lafiya suka yi suka rasu a cewar shugabar hukumar ta Rwanda Nirere Madeleine.

Kasar ta Ruwanda dai ta saba karyata rahotanni na kungiyoyin kare hakkin bil Adama ciki kuwa har da batun yadda jami'an tsaro ke gallazawa mutanen da ke tsare a hannunsu.